Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An rusa su mako guda bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta kara wa’adin shugabanninsu da watanni biyu

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rusa shugabannin riko na kananan hukumomi 44 da ke jihar tare da mika ragamar jagorancin ga daraktocin kula da ma’aikata.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani taro na musamman da aka gudanar a dakin taro na Africa House da ke gidan gwamnatin Kano.

Wannan na zuwa ne mako guda bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta amince da karin wa’adin shugabannin rikon da watanni biyu, wanda tun da farko zai kare a ranar 8 ga Satumba, 2024.

“Wannan rushewar ta shafi dukkan shugabanni, mataimakan shugabanni, sakatarori, da kansiloli.

“Muna gargadin DPMs da su tabbatar ba za su tsoma baki cikin duk wata harka ta siyasa ba, a matsayinsu na ma’aikatan gwamnati,” in ji gwamnan.

Gwamnan ya nuna godiya ga shugabannin rikon bisa gudunmawar da suka bayar wajen cigaban yankunansu, ya kuma yi nuni da cewa akwai yiwuwar yin aiki da su nan gaba.

Su kuma shuwagabannin riko sun godewa gwamnan bisa damar da ya basu na yiwa al’ummarsu hidima.