Kano: An kama Daraktan ma’aikatar ruwa kan karkatar da injinan rarraba ruwa

’Yan sanda sun tsare Daraktan Ma’aikatar Ruwa ta Kano kan zargin karkatar da injinan rarraba ruwan sha a jihar.

Kano: An kama Daraktan ma’aikatar ruwa kan karkatar da injinan rarraba ruwa

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Hussaini Muhammad Gume,

’Yan sanda sun tsare Daraktan Ma’aikatar Ruwa ta Kano kan zargin karkatar da injinan rarraba ruwan sha a jihar.

An tsare Daraktan Gudanarwa da Ayyuka na ma’ikatar Abubakar Gambo ya shiga hannun ’yan sanda ne tare da wasu mutane biyu kan zargin su da yin takardun bogi na smaun izinin yi gwanjon wasu manyan injinan rarraba ruwan sha da kuma tankuna.

Kwamishinan ’an sandan jihar, Hussaini Muhammad Gumel, ya ce mutanen sun shiga hannun ne bayan Kwamishinan Ruwa na jihar, Ali Makoda, ya musanta ba da izinin sayar da injinna ruwan da kuma tankuna, yana mai cewa tsantar damfara ce suka shirya.

Hussaini Gumelya ce rundunarsa na ci gaba da bincike kan lamarin domin gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya.

Ya shaida wa wakilinmu cewa sauran wadanda aka kama su ne Mataimakin Sakataren Gudanarwa, Baba Yahaya da kuma Nuhu Mansir, wanda sohon Manajna Shirin Noman Rani a  KAREFA ne a Karamar Hukumar Tudun Wada.

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara