Kano: Ba zan rika yi wa gwamnatin Abba katsa-landan ba – Kwankwaso
Kwankwaso ya ce ko kadan ba zai yi wa Abba katsa-landan ba a mulkinsa
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya karyata zargin da mutane ke yi cewa ba zai kyale zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gudanar da gwamnatinsa ba tare da sa hannunsa ba.
Kwankwaso ya ce ba shi da wani shirin yi wa sabuwar gwamnatin ta Kano katsalandan a cikin ayyukanta.
- Jiragen sojin Amurka 2 sun yi hatsari suna tsaka da sintiri
- Mamallakin Manchester City ya zama Mataimakin Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa
Tsohon Gwamnan na Kanon ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da maneman labarai a Jihar Kano ranar Laraba.
A cewarsa, akwai abubuwan da za a iya ba wa shugabannin shawara akwai kuma wuraren da za a kyale su, su yi ayyukansu da kansu.
“Dole ne a bar shugabanni su yi aikinsu da kansu su zartar da abubuwan da suke na tunaninsu. Duk da cewa akwai ’yan abubuwan da ba za a rasa bayar da shawara a kansu ba. Za a iya daukar shawara ko kuma ma a yi watsi da ita, ba dole ba ne a ce sai an dauke ta ba.”
Kwankwaso ya kuma ce yana da yakinin cewa sabuwar gwamnatin ba za ta ki yin amfani da shawara ba matukar tana kan hanya.
“Muna da tabbacin wannan Gwamnan da Mataimakinsa ba za su ki bin shawara ba, ba kamar wannan gwamantin da ta ki bin shawarwarin jama’a ba,” in ji Kwankwaso.
Ya bayyana cewa qin yin amfani da shawarwari da Gwamnan Ganduje ya yi shi ya kai gwamnatinsa ga faxa wa hlin da ake ciki a yanzu
“Shi ma Ganduje ya ki yin amfani da shawarwarin da ake ba shi ne shi ya sa ya shiga halaka, ya sa gwamantinsa ta fada halin da take ciki a yau. Wannan halakar da ya shiga ta rika bin sa ke nan har abada,” in ji Kwankwaso.