Kano: Babu saki tsakanin masu auren gata sai da izinin Hisbah — Daurawa
Kwamandan hukumar ya ce sun yi tanadin yadda za a warware matsala a tsakiyar waɗanda za a yi wa auren.
Shiekh Aminu Daurawa
Babban Kwamandan Hukumar Hisbah na Jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi gargaɗin cewa babu tsaki tsakanin masoyan da gwamnati ta shirya yi wa auren gata sai da sahalewar hukumar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara hedikwatar hukumar da ke sanya ido kan cuta mai karya garkuwar jiki ta jihar (KSACA), inda ake tantance lafiyar waɗanda za su ci gajiyar shirin.
Daurawa, ya ce gwamnati ta shirya sosai domin tabbatar da shirin kuma tana sa ran auren zai yi ƙarko.
“Ba ma bari a yi saki. Duk wanda saboda wani dalili yake son saki sai ya dawo Hisbah tun da a nan aka ɗaura auren. Muna da kwamitin sulhu da aikinsa ne warware matsalolin ma’aurata kafin a kai ga saki,” in ji shi.
Daurawa, ya ƙara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yanke shawarar yin auren gatan ne domin sauƙaƙawa talakawan da ke son aure amma ba su da ƙarfi.
“Wasu suna sayar da ababen hawansu, wasu filayensu, wasu ma bashin banki suke karɓa duk don su yi aure.
“Wannan ne ya sanya Gwamna ya yanke shawarar aurar da masoya 1,500. Gwamnatin ce za ta yi musu kayan ɗaki, akwatinan lefe, sutura, da abinci.”
“Haka kuma dukkanin masoyan za su samu kyautar Naira 200,000, Naira 100,000 a matsayin sadaki, da kuma Naira 100,000 a matsayin jari.
“Za a ƙara musu da shinkafa, taliya, da kuma man girki. Wannan tanadin kusan na Naira 250,000 ne.” In ji Daurawa.
Kwamandan ya ce da dama daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin a baya sun hayayyafa, inda wasu a ciki suka sanya sunan gwamnan Kano domin nuna godiyarsu.
A nasa ɓangaren shugaban hukumar KSACA, Usman Bashir, ya ce tantancewar na daga cikin tanadin dokar lafiya ta 2024.
“Muna aikin tantance mutum 3,000 domin tabbatar da ingancin lafiyarsu kafin aure. Idan muka kammala za mu ba su takardar shaida. Waɗanda kuma ke da wata larura kamar ta sikila za mu ba su shawarar haƙura da juna.
“Gwamnatin ce ta ɗauki nauyin komai. Don haka duk wanda buƙatar magani za a yi masa.”