Kano da Filato: Jiran hukuncin kotun daukaka kara ya kawo fargaba

Manyan ’yan siyasa da magoya baya sun shiga fargaba a jihohin Kano da Filato a yayin da ake jiran hukuncin kotun daukaka kara kan zaben gwamnonin jihohin

Kano da Filato: Jiran hukuncin kotun daukaka kara ya kawo fargaba

Manyan ’yan siyasa da magoya baya sun shiga fargaba a jihohin Kano da Filato a yayin da ake jiran hukuncin kotun daukaka kara kan zaben gwamnoni da ’yan majalisar jihohin biyu.

Idan ba a manta ba, a baya kotun sauraron kararrakin zabe ta tsige Abba Kabir Yusu na Jam’iyyar NNPP tare da ayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano.

A Filato kuwa, kotu ta tabbatar da zaben gwamnan jihar, Caleb Mutfwang na Jam’iyyar PDP, amma ta kori dukkanin ’yan majalisar dokokin jihar na jam’iyyar, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a jihar.

Sai dai hukuncin da kotunan suka yanke a jihohin biyu ya haifar da taraddadin abin da ka iya zuwa ya dawo.

Wannan dalili ne ya sanya Rundunar ‘Yan Sandan Jihar  Kano ta lashi takobin tabbatar da zaman lafiya da tsaron jama’a gabanin hukuncin kotun daukaka kara da ake tsimaye kafin karshen wannan mako.

Rundunar ta kuma sanya dokar hana duk wani taron siyasa, zanga-zanga ko taron murna bayan bayyana hukuncin kotun.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Usaini Gumel, ya bai wa al’ummar Kano tabbacin samun isasshen tsaro kafin da kuma bayan yanke hukuncin,  inda ya bukaci ’yan siyasa da su guji furta kalaman da za su iya harzua jama’a.

Mazauna jihohin biyu sun shaida wa Aminiya cewa, duk da cewa za a yanke hukuncin a Abuja, amma rashin sanin ainihin ranar ya sanya su cikin fargaba.

Filato

Sabanin wasu jihohin da kotun daukaka kara ta kori ’yan majalisa daya ko biyu na jam’iyyun siyasa ba, kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta kori duka ’yan majalisar PDP bakwai a matakin kasa — sanatoci uku da ’yan Majalisar Wakilai biyar — da suka fito daga jihar Filato.

A hukuncin kotun baya da ta kwace kujerun ’yan majalisar na PDP, kotun ta ce duk wadanda suka shiga zabukan a PDP ’yan takara ne masu zaman kansu, wanda hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Wannan hukunci ya haifar da fargaba da zanga-zanga a jihar.

Kano

A Kano kuwa magoya bayan jam’iyyar NNPP na burin ganin kotun dukaka kara ta dawo da ’yan majalisar PDP uku da kotun sauraron kararrakin zabe ta kora.

Kazalika, Hassan Fagge, mai taimaka wa dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce, “Bisa ga hujjojin da aka gabatar a gaban kotun da kuma hukuncin da ta yanke, nasara tamu ce da ikon Allah a kotun daukaka kara.”

A Jihar Filato, Simon Venmak Gomla, shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar Filato ta Kudu, ya ce yana da yakinin za su samu nasara a kotun daukaka kara duk da hukuncin da aka yanke wa mambobin jam’iyyarsa a baya.

Sai dai sakataren yada labarai na APC, Sylvanus Namang, ya ce tunanin samun nasara da PDP ke yi ba komai ba ne face yaudarar kai.