Kano: Dalilin da ya sa na ziyarci Sanatan NDC — Nentawe
Shugaban ya ce sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi makomar Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce ziyarar da ya kai wa Sanata Rufai Hanga na jam’iyyar NDC, ta ta’allaƙa ne kan batun inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Kano.
Yilwatda, ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis bayan ya kai wa Sanata Hanga ziyara.
- Amurka za ta sayar wa Saudiyya makaman dala biliyan 1.96
- Boka ne ya ba ni umarnin kashe ƙanwar mahaifina da ’ya’yanta 6 — Umar
Ya bayyana Sanata Hanga a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin NDC a Jihar Kano.
Ya ce tattaunawar da suka yi ta mayar da hankali ne kan haɗin kai, zaman lafiya, kwanciyar hankali da makomar Jihar Kano.
“Tattaunawar da muka yi ta gudana cikin fahimtar juna, kuma ta fi mayar da hankali kan haɗin kai, zaman lafiya, kwanciyar hankali da makomar Jihar Kano,” in ji Yilwatda.
Shugaban na APC ya ce bambancin jam’iyya bai kamata ya hana shugabanni yin aiki tare domin amfanar al’umma ba.
“Ko mutum yana wata jam’iyya daban, shugabanni suna da alhakin tabbatar da zaman lafiya, ƙarfafa dimokuraɗiyya da yin aiki tare domin amfanar jama’a,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa Najeriya za ta samu ci gaba idan shugabanni suka zaɓi tattaunawa da haɗin kai maimakon rarrabuwar siyasa.
“Najeriya za ta fi samun ci gaba idan muka gina gadar fahimtar juna, muka ƙarfafa tattaunawa mai amfani, sannan muka fifita jin daɗin “yan ƙasa fiye da muradun jam’iyya,‚ in ji Yilwatda.
Yilwatda, ya yi fatan cewa haɗin gwiwar shugabannin siyasa zai taimaka wajen gina Kano da Najeriya ta hanyar samun haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba.