Kano: EFCC ta kama mutum 280 a cikin shekarar 2019

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, (EFCC) reshen jihar Kano, ta ce ta kama mutum 280 a jihar, wadanda suke da alaka da cin hanci da rashawa daga watan Janairu zuwa Agusta na wannan shekarar 2019. Shugaban hukumar EFCC reshen jihar Kano, Mista Akaninyene Ezima ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya […]

Kano: EFCC ta kama mutum 280 a cikin shekarar 2019

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, (EFCC) reshen jihar Kano, ta ce ta kama mutum 280 a jihar, wadanda suke da alaka da cin hanci da rashawa daga watan Janairu zuwa Agusta na wannan shekarar 2019.

Shugaban hukumar EFCC reshen jihar Kano, Mista Akaninyene Ezima ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce an kama mutanen da laifuka daban-daban, wanda suka hada da kutse cikin yanar gizo-gizo, satar kudade da dai sauransu.

Akaninyene, ya kara da cewa hukumar ta EFCC ta karbo kudade sama da Naira miliyan 550, da kuma kudin dalar Amurka dubu 690, sai dai ya ce hukumar ta kama dalolin ne a tashar tashi da saukar jirage ta Malam Aminu Kano (MAKIA).

A karshe ya yi kira ga bankuna da su kara tsananta tsaro da kuma kula da ayyukansu don ganin masu kutse ta yanar gizo basu saci kudaden al’umma ba.