Kano: Gobara ta cinye daruruwan shaguna a Kasuwar Gwarzo

Daruruwan ’yan kasuwa sun yi asarar kadarorinsu a wata gobara da ta tashi a kasuwar garin Gwarzo da ke Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano.

Kano: Gobara ta cinye daruruwan shaguna a Kasuwar Gwarzo

Wata gobara da ta tashi (tsohuwar ajiya)

Daruruwan ’yan kasuwa ne suka yi asarar kadarori na miliyoyin Naira a wata gobara da ta tashi a kasuwar garin Gwarzo da ke Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano.

Gobarar ta ranar Litinin ta jefa ’yan kasuwa cikin rudani, inda wasunsu suka yi ta kokawa kan asarar babbar jarinsu.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce gobarar ta kone shaguna da dama ta lalata dukiyoyin miliyoyi na Naira, amma ba a samu asarar rai ko wanda ya ji rauni ba.

Ya bayyana cewa, gobarar ta tashi ne da tsakar daren Lahadi kuma sai dai jami’ansu sukai kai safiyar Litinin suna aiki kafin su kashe ta.

Daya daga cikin ’yan kasuwar da suka yi asara, Dayyabu Lawan Bala ya ce ya yi asarar kadarori na sama da miliyan biyar, ciki har da shagon.

Ya yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su kawo musu dauki domin rage musu radadin asarar da suka yi.

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka

Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji