Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu

“Rayukan mutane bakwai ne suka salwanta sakamakon wata gobara da ta tashi yayin da kuma aka ceto rayukan mutum bakwai.”

Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu

Jami’an Kashe gobara

Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da kadarori na sama da Naira miliyan 50 suka salwanta sanadiyyar gobarar a cikin watan Fabrairun 2025 a Jihar Kano.

Kakakin hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar.

Ya ce, a cikin watan Fabrairu, 2025, hukumar kashe gobara ta jihar ta samu jimillar kiraye-kirayen lambar wayar kashe gobara 77, da lambar kiran neman ceto 11 da kuma ƙararrakin gobara na ƙarya uku.

“Kimanin kadarori da gobara ta lalata a cikin watan Fabrairu sun kai darajar kuɗi N50,318,000 yayin da ƙiyasin kadarorin da jami’an kashe gobara na jihar suka ceto sun kai N180,318,000.

“Rayukan mutane bakwai ne suka salwanta sakamakon wata gobara da ta tashi yayin da kuma aka ceto rayukan mutum bakwai.”

Hukumar ta yi kira ga jama’a da su riƙa kula da wuta cikin kulawa domin gujewa afkuwar gobara yayin da aka shawarci masu ababen hawa da su riƙa tuka mota cikin kulawa tare da bin dokar hanya musamman a lokacin da suke tafiya kan manyan hanyoyi domin guje wa haɗurran mota.