Kano: Ka da ku biya ko ficika don yin auren gata — Hisba

Hukumar ta gargaɗi masu son yin rajistar shirin da su yi taka-tsan-tsan.

Kano: Ka da ku biya ko ficika don yin auren gata — Hisba

Hukumar Hisba ta Jihar Kano, ta gargaɗi mutane kan biyan kuɗi da sunan yin rajistar auren gata da gwamnatin jihar za ta gudanar kwanan nan.

Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dokta Mujahideen Aminuddeen ne, ya yi gargaɗin a ranar Laraba.

Ya ce hukumar ta samu rahotannin da ke nuna wasu mutane na karɓar kuɗi hannun waɗanda za su ci gajiyar shirin, duk da cewa gwamnati ta ɗauki nauyin aiwatar da shirin.

Dokta Aminuddeen, ya sake tabbatar da cewa babu wanda hukumar da kuma gwamnatin jihar suka wakilta domin karɓar kuɗin yin rajistar shiga shirin.

Ya kuma yi bayanin cewa Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya amince da ɗaukar nauyin suturar masu cin gajiyar shirin, da kayan ɗaki, da kuɗin mota, da kuma ba su jari kyauta.

Ya kuma ja hankalin al’umma da su shigar da ƙorafin duk wani wanda ya nemi kuɗi a wajensu ga hukumar da kuma hukumomin tsaro domin bincike da kuma ɗaukar mataki daidai da doka.

Aminiya ta ruwaito cewa gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 1.5 domin shirin aurar da mutane 1,500 a jihar, ƙarƙashin hukumar ta Hisba.