Kano: Mun gano badakalar kudin taki ta biliyan 4 a gwamnatin Ganduje – Muhuyi
Hukumar ta ce tuni ta kama mutum 8 a kan lamarin
Hukumar Karbar Koke-koke da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano ta ce ta gano wata badakalar kudin takin zamani ta Naira biliyan hudu da ta zargi jami’an gwamnatin da ta gabata da karkatarwa.
Hukumar ta ce an karkatar da kudaden ne daga asusun Kamfanin Samar da Kayan Amfanin Gona na Jihar (KASCO), zamanin tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje.
Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a Kano ranar Asabar.
Ya ce sun samu nasarar gano badakalar ce lokacin da ya jagoranci wani bincike da suka gudanar a kan dakin adana kayayyaki na kamfanin.
Muhuyi ya kuma ce tuni suka kama mutum takwas da ake zargin suna da hannu a cikin badakalar, inda ya ce tuni har sun fara bincike domin gano hanyar da aka bi aka karkatar da kudaden.
Sai dai ya ce sun gano wasu motoci da taraktoci a wani waje da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar, wadanda aka yi amannar cewa da irin kudaden aka sayo su.
Muhuyi ya yi zargin cewa an sayo kayayyakin ne da kudaden da aka karkatar daga lalitar gwamnati, amma aka kai su wata kungiya mai rajista da Hukumar Kula da yi wa Kamfanoni Rajista (CAC) mai suna ‘Association of Compassionate Friends’.
Ya kuma ce, “An kafa kungiyar ce da nufin tallafa wa kananan yara da kuma marasa galihu a cikin al’umma, amma sai aka bige da amfani da ita wajen satar kudin gwamnati.
“Tuni mun kama mutum takwas da muke zargi da hannu dumu-dumu a ciki, kuma tuni sun fara ba mu ingantattun bayanai. Daya daga cikinsu ya ce wani adadi na kudin domin yin wata cuwa-cuwa ta karya, amma ya ajiye su bai taba ba, saboda tsoron rana irin wannan. Ya riga ma ya dawo da kudin yanzu haka,” in ji Muhuyi.