‘Kano na bukatar biliyan 6 don samar da kujeru a makarantu’
Kwamishinan ilimin jihar ya bukaci a tallafawa bangaren don yi masa garambawul.
Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana bukatar akalla Naira biliyan shida don wadata makarantun firamare da sakandare 9,063 na jihar da kujerun zama.
Kwamishinan Ilimin Jihar, Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jami’an hukumar UNICEF a Kano, karkashin jagorancin Shugaban ofishin a Kano, Rahama Mohammad Farah, a ofishinsa.
- An tashi kunnen doki a wasan ’yan sanda da tubabbun ’yan daba a Kano
- Najeriya ta yanke wutar lantarkin da take ba wa Nijar
Ya ce, kididdigar na zuwa ne biyo bayan mummunan yanayi da fannin ilimi ya samu kansa, wanda hakan ya sa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya umarci ma’aikatar ilimi ta tantance adadin kayan aikin makarantun ke bukata.
“Mun gano cewa yara miliyan 5.2 a makarantunmu ba su da kujeru da tebura. Hasali ma, a wata ziyara da na kai, na tarar da wata makaranta mai suna Dawanau Special Primary School da ke karamar hukumar Dawakin Tofa, da dalibai 5,618 duk suna zaune a kasa! Kun ga yadda lamarin ya yi muni,” in ji shi.
Ya kara da cewa baya ga rashin kujeru, sauran matsalolin da ke addabar makarantun sun hada da rashin ababen more rayuwa, kayan amfanin malamai, da kuma matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, wanda ya kai ga rugujewar tsarin ilimi gaba daya.
“Na ji dadi da na ziyarci wasu makarantun. Na ziyarci makarantar da ke da yara sama da 500, wadda ma’aikaci daya ne ke aiki a matsayin babban malami. Bai kamata hakan yake faruwa a cikin al’ummar da ke muradin ci gaba ba”.
Doguwa, ya jaddada cewa Kano tana da kalubale musamman a fannin ilimi, saboda yadda harkar ta tabarbare, amma ya jaddada bukatar masu kishin kasa su marawa gwamnatin jihar baya wajen ganin an yi wa harkar garambawul.
Kwamishinan, ya bukaci masu ruwa da tsaki da su daidaita abubuwan da suka sa a gaba a fannin ilimi da na gwamnatin jihar, don tunkarar kalubalen da ke damun su.
Tun da farko, shugabar ofishin UNICEF a Najeriya, Misis Rahama Rihood Mohammad Farah ta sabunta kudirin UNICEF na yin aiki tare da gwamnatin jihar.
Ta bayyana abubuwan da hukumar ta sa gaba a fannin ilimi, ciki har da tallafawa ci gaban shirin ilimi na shekara hudu ga jihar.