Kano: Na kusa tona asirin maciya amana —Bichi

Sakataren Gwamnatin Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sallama, Abdullahi Baffa Bichi ya ce nan gaba kaɗan zai tona asirin maciya amana a jihar.

Kano: Na kusa tona asirin maciya amana —Bichi

Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sallama, Abdullahi Baffa Bichi ya ce nan gaba kaɗan zai tona asirin maciya amana a jihar.

A wani bidiyon Abdullahi Baffa Bichi a yayin da yake jawabi ga magoya bayansa, an ji shi yana cewa nan gaba kaɗan zai yi tonon silili.

Tun bayan sallamar Baffa Bichi daga aiki ba a’a sake jin ɗuriyarsa ba. Gwamna Abba ya sallame shi ne tare da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Shehu Wada Sagagi, da wasu kwamishinoni biyar.

Sai dai kuma daga bisani aka naɗa Sagagi Kwamishinan Kasuwanci da Zuba Jari, tsohuwar Kwamishinar Raya Al’adu da Yawon Bude Ido, Ladidi Garko kuma aka naɗa ta Shugabar Ma’aikatan Jihar Kano.

Bichi, ya ce, “Na gama aiki lafiya.  Yanzu ba lokacin surutu ba ne, amma akwai abubuwa da yawa da za a fa. Akwai abubuwa da yawa a rubuce, a cikin sauti da bidiyo.

“Allah Ya jarrabe mu da marasa  rikon amana; lokaci zai zo da za mu fito da abubuwa don mutane su ji su gane su wane ne. Ba waɗanda za a aminta da su ba ne, babu abin da suka iya sai yaudara da cin amana.

“Na gode wa mutanen Bichi, za ku ji daga gare mu nan da wani lokaci kaɗan domin abin da muke so shi ne mu taimaka wa mutane.”

Ana zargin Abdullahi Baffa Bichi ne ya assasa ƙungiyar ‘Abba Tsaya da Kafarka’ da ke neman gwamnan ya samu yancin kai daga ubangidansa na siyasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Bichi, wanda jigo ne a tafiyar Kwankwasiyya, ya taka rawar gani a zaben 2023 wanda ya kai ga nasarar Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano.