Kano ne birni mafi gurbacewar iska a Afirka – Rahoto
A wani bincike da aka gudanar, an gano cewa birnin Kano ne birni mafi gurbacewar iska a Afirka, inda gurbacewar iskar ta kai kashi 53.4 cikin dari. Rahoton ya bayyana amfani da itace da kananziri da gawayi yayin girki da dagwalo da sharar gona da hayakin ababan hawa a matsayin abubuwan da suke gurbata muhalli. Rahoton […]
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
A wani bincike da aka gudanar, an gano cewa birnin Kano ne birni mafi gurbacewar iska a Afirka, inda gurbacewar iskar ta kai kashi 53.4 cikin dari.
Rahoton ya bayyana amfani da itace da kananziri da gawayi yayin girki da dagwalo da sharar gona da hayakin ababan hawa a matsayin abubuwan da suke gurbata muhalli.
Rahoton ya nuna cewa birnin Kampala ne ke biye da na Kano a gurbacewar iskar, inda birnin Fatakwal na Najeriya ya zama na uku sannan birnin Adis Ababa ya zamo na hudu a jadawalin birane masu mafi gurbatacciyar iskar.
Da farko dai rahoton wanda cibiyar IK Airbisual mai hedkwata a kasar Switzerland ta fitar, ya sanya Najeriya a matsayin kasa ta 10 mafi gurbacewar yanayi a duniya.
Rahoton ya ce gurbatacciyar iska da ke Najeriya ta kai kashi 44.8 cikin 100, inda Uganda da Habasha suke biye da ita, kamar yadda BBC ya ruwaito.
Rahoton na cibiyar IK Airbisual ya ce Nahiyar Afirka na fama da rashin hanyar tattara bayanan bibiyar iska mai inganci, yayin da kuma take fuskantar kalubalen gurbacewar iska masu alaka da ita kanta nahiyar.
Ya ce Afirka na da bunkasar birane mafiya sauri ga kuma karuwar jama’a da ke kwarara zuwa manyan birane, inda gurbatacciyar iska ta fi yawa.