Kano Pillars na ƙoƙarin gyara kafin sabuwar kaka
Tun da Pillars ta dawo Firimiyar Nijieriya har yanzu ba ta dawo ganiyarta ba.
A ranar Talatar da ta gabata ce Ƙungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta sanar da ɗaukar Usman Abdallah a matsayin sabon kocinta.
A ranar ce aka gabatar da sabon kocin, inda ya zo domin kokarin dawo da martabar kungiyar, wadda ta kwana biyu tana fama da kwangaba-kwan-baya.
- ‘Yan wasa 20 da ke fama da rauni kafin fara Firimiyar Ingila
- City ta doke United a kofin Community Shield
Haziƙin kocin ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar shekara biyu da kuma yiwuwar ƙarin wata shekarar, domin jagorantar Sai Masu Gida.
Usman Abdullah, yana da gogewa a harkar ƙwallon ƙafa, inda ya taɓa zama mataimakin kocin ’yan ƙwallon Super Eagles.
Ya samu gagarumar nasara a Kungiyar Eyimba International FC, inda ya lashe gasar Firimiyar Nijeriya.
Kazalika, ya taka rawar gani a Kungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourist da ke Bauchi kuma Katsina United.
Abdallah yana da lasisin koyarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA), wanda hakan ya nuna irin gogewar da yake da ita a harkar.
Kano Pillars za ta fara kakar wasanni ta 2024/2025 a gida, inda za ta karɓi baƙuncin sabuwar Kungiyar Ikorodu City of Legas.
Abdallah ya maye gurbin Offor Paul, wanda aka nada sabon kocin kungiyar, amma ya raba gari da kungiyar a kasa da wata biyu, inda aka yi rabuwar mutunci.
Aminiya ta ruwaito cewa Kungiyar Kano Pillars ta fara samun koma-baya ne a karshen kakar shekarar 2021/2022, inda ta kasance cikin kungiyoyi uku da suka koma gasar baya, wato NNL, tare da kungiyoyin Heartland da Katsina United.
Sai dai kungiyar ta dawo babbar gasar kasa, ta Firimiyar Nijeriya, amma tun da ta dawo, har yanzu ba ta dawo ganiyarta ba.
Idan ba a manta ba, a watan jiya ne Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin sababbin shugabannin ƙungiyar ta Kano, Pillars a karkashin jagorancin Aliyu Nayara Mai Samba.
An nada sababbin shugabannin kungiyar ce tun bayan da aka kori Babangida Little da kwamitinsa daga jagorancinta.
A wata sanarwa da aka fitar daga ofishin Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabi’u Kwankwaso ta sanar da nada mutum 14 da za su ja ragamar Pillars.
Ali Nayara Mai Samba shi ne sabon shugaba a matakin rikon kwarya na shekara ɗaya.
Daga cikin kwamitin akwai fitaccen mai sharhi a kan wasanni, wato Abubakar Isa Dandago a matsayin jami’in watsa labaran ƙungiyar.
Kano Pillars ta kare a mataki na 11 a Gasar Firimiyar Nijeriya da ta wuce, kuma tana fatar taka rawar gani a kakar 2024/2025.
Za dai a fara Gasar Firimiyar Nijeriya ce a ranar 31 ga Agustan nan, inda aka tanadi Naira miliyan 200 ga duk kungiyar ta lashe kofin a bana.