Kano Pillars na makokin dan wasanta Bello Kofar-Mata
Marigayin dai ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya.
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta aike da sakon ta’aziyar rasuwar fitaccen dan wasan kungiyar da kuma El-Kanemi Warriors, Musa Bello Kofar-Mata a ranar Talata.
Cikin sanarwa daban-daban da Kano Pillars hadi da El-Kanemi Warriors suka fitar ne suka bayyana kaduwarsu da rasuwar tare da addu’ar Allah ya jikan sa, ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure rashinsa.
- Saudiyya ta daure mutum 11 shekara 65 saboda wadaka da dukiyar gwamnati
- Zaben 2023: CAN ta ayyana ranar yi wa Najeriya addu’a
Wani makusancin margayin dai ya bayyana wa Aminiya cewa tuni an binne shi a safiyar ranar Laraba, bayan rasuwarsa cikin dare a sakamakon wata ’yar takaitacciyar jinya.
Bello Kofar-Mata ya fara kwallon kafa ne a kungiyar kwallon kafa ta Buffalos FC kafin komawa Kano Pillars, inda ya samu nasarar lashe kofin Firimiyar Najeriya (NPFL) a shekarun 2007 da 2008.
Dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga a gasar NPFL din ya wakilci Najeriya a Gasar Kofin Duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 da aka yi a Canada a shekarar 2007.
Marigayin ya fara buga wa babbar kungiyar a shekarar 2010, a wasan da suka lashe da ci 5-2 da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.
Ana iya tunawa cewa, a shekarar 2007 ne Kofa-Mata ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta IK Start ta kasar Norway, kafin zuwansa LASK ta Australiya a 2008 a matsayin dan wasan aro.
Marigayin dai ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya.