Kano Pillars ta doke Katsina United a Firimiyar Najeriya
Ahmed Musa ne ya ci ƙwallon daf da tashi a karawar da suka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata a Jihar Kano.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta yi nasarar doke Katsina United 1-0 ranar Laraba a wasan mako na 23 a gasar Firimiya ta Najeriya.
Ahmed Musa ne ya ci ƙwallon daf da tashi a karawar da suka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata a Jihar Kano.
- Inganta Tattalin Arziki: An ƙaddamar da sabbin kayan bunƙasa kiwo
- An yi wa wata mai shekara 70 fyaɗe a Kaduna
A haɗuwar ƙarshe da ƙungiyoyin biyu suka yi a cikin watan Satumban bara, Katsina United ce ta ci Kano Pillars 1-0 a babbar gasar tamaula ta Najeriya.
Da wannan sakamakon ƙungiyar Pillars da ake laƙabi da ‘Sai Masu Gida’ ta koma mataki na 18 a teburin Firimiyar ta Najeriya da maki 25.
Ita kuwa Katsina United mai maki 30 tana mataki na 11, amma tana da kwantan wasan a hannu.