Kano Pillars ta gabatar da Abdallah a matsayin sabon kocinta 

Wannan na zuwa ne bayan da Gwamnatin Kano ta yi wa ƙungiyar garambawul.

Kano Pillars ta gabatar da Abdallah a matsayin sabon kocinta 

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da ɗaukar Usman Abdallah a matsayin sabon kocinta.

Haziƙin kocin ya rattaba hannun yarjejeniyar shekara biyu da kuma yiwuwar ƙarin wata shekarar, domin jagorantar Sai Masu Gida.

Aminiya ta ruwaito cewar Usman Abdullah, yana da gogewa a harkar ƙwallon ƙafa, inda ya taɓa zama mataimaki a tawagar ‘yan ƙwallon Super Eagles.

Ya samu gagarumar nasara a ƙungiyar Eyimba International FC, inda ya lashe gasar Firimiyar Najeriya.

Kazalika, ya taka rawar gani a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wikki Tourist da kuma Katsina United.

Abdallah yana da lasisin koyarwa na hukumar ƙwallon ƙafa ta UEFA, wanda hakan ya nuna irin gogewar da yake da ita a harkar.

Kano Pillars za ta fara kakar wasanni ta 2024/2025 a gida, inda za ta karɓi baƙuncin sabuwar ƙungiyar Ikorodu City of Lagos.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS