Kano Pillars ta lallasa 3SC a Kano
Kulob din Kano Pillars da aka fi sani da “Sai Masu Gida” ya lallasa kulob din 3SC na Ibadan da ci 4-1 a ranar Lahadin da ta wuce a gasar rukunin firimiya na Najeriya (NPFL) mako na 23.’Yan kwallon da suka zura wa Pillars kwallo a raga sun hada da Rabi’u Ali da Ubong Ekpai […]
Kulob din Kano Pillars da aka fi sani da “Sai Masu Gida” ya lallasa kulob din 3SC na Ibadan da ci 4-1 a ranar Lahadin da ta wuce a gasar rukunin firimiya na Najeriya (NPFL) mako na 23.
’Yan kwallon da suka zura wa Pillars kwallo a raga sun hada da Rabi’u Ali da Ubong Ekpai da Tony Edjomarigwe da kuma Adamu Mohammed. dan kwallon 3SC Ajani Ibrahim ne ya zura kwallo daya tilo a ragar Pillars.
Ya zuwa shekaranjiya Laraba Pillars ita ce ta biyar a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar bayan ta hada maki 37 daga wasanni 23.
Kulob din Sunshine Stars na Akure ne ke saman tebur a gasar da maki 43 sai Enyimba na Aba ke biye da maki 42 sai Warri Wolbes a matsayin ta uku da maki 40 sai Wikki Tourist na Bauchi da maki 38 yayin da Pillars take matsayi na biyar da maki 37.