Kano Pillars ta naɗa sabon mai horaswa
Paul Offor shi ne tsohon kocin Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Sporting Lagos.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars ta naɗa Paul Offor a matsayin sabon kocin ƙungiyar.
Sabon naɗin na zuwa ne bayan raba gari da Abdu Maikaba da ƙungiyar ta yi a ƙarshen kakar wasanni ta 2024 saboda rashin katabus.
- Dalilai uku da ke janyo rikici tsakanin ’yan siyasa da sarakuna
- ’Yan ta’adda sun tsere daga gidan yarin Nijar
Paul Offor dai tsohon mai horas da Ƙungiyar Kwallon Ƙafa ta Sporting Lagos ne wanda ya taka rawar gani a kakar wasan da ta gabata.
Shugaban Kungiyar ta Kano Pillars Babangida Umar Little, shi ne ya jagoranci ƙaddamar da Offor a babban ɗakin taro na Kabo Guest Inn da ke birnin Kano.
Babangida ya bayyana wa manema labarai cewa Offor Paul zai kawo wa ƙungiyar ta Kano Pillars ci gaba, kuma za su ba shi dukkan haɗin kan da ya dace don ganin sun lashe gasar ajin ƙwararru ta kasa wato Premier League.
Sannan ya yi kira ga magoya bayan Pillars da su taya ƙungiyar da addu’a don samun nasarar ƙungiyar.
An rushe kwamitin riƙon Kano Pillars
Kazalika, Gwamnatin ta rushe kwamitin riƙo na hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars wanda Alhaji Babangida Umar Little ke jagoranta.
Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Wasanni da Ci gaban Matasa na jihar, Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce an rushe kwamitin ne a dalilin ƙarewar da wa’adinsa ya yi tun a watan Disamba na 2023.
Sanawar ta bukaci shugabanin da aka rushe da su mika shugabancin gudanarwar kungiyar ga ma’aikacin gwamnati mafi girma a hukumar kafin a nada sabbin shugabanni.
Kwankwaso a madadin Gwamnatin Kano yaba wa shugabanin masu barin gado kan gudunmawar da suka bayar da kuma rawar da suka taka a tsawon wa’adin da suka yi na ciyar da Kano Pillars gaba.
Ya bayar da tabbacin cewar gwamnatin jiha za ta cigaba da bai wa kungiyar ta Kano Pillars kulawar da ta kamata.