Kano Pillars za ta ci gaba da rike kambinta – Kabiru Baita
Duk da rashin nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi a yammacin Litinin da ta gabata a hannun takwararta ta Sharks da ke garin Fatakwal da ci daya mai ban haushi, sabon shugaban kungiyar ta Kano Pillars, Alhaji Kabiru Baita ya ce suna da karfin gwiwar kungiyar za ta farfado ta sake […]
Duk da rashin nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi a yammacin Litinin da ta gabata a hannun takwararta ta Sharks da ke garin Fatakwal da ci daya mai ban haushi, sabon shugaban kungiyar ta Kano Pillars, Alhaji Kabiru Baita ya ce suna da karfin gwiwar kungiyar za ta farfado ta sake rike kambinta a gasar Premier.
Alhaji Kabiru Baita ya shaida wa wakilinmu cewa nasarar da kungiyar ta Sharks ta samu a kan Kano Pillars haka yanayin wasa yake zuwa, inda ya ce ’yan wasansa sun yi matukar kokari a fafatawar da suka yi, kuma duk wanda ya kalli wasan ya tabbatar da haka.
Ya ce kungiyar Kano Pillars ta zamo abar misali a cikin kungiyoyin kwallon kafa na kasar nan da Nahiyar Afirka, inda ta dauki kofin Premier sau uku a jere, kuma hakan wani lamari ne mai muhimmanci a tarihin gasar da ta Nahiyar Afirka.
Ya jinjina wa ’yan wasan saboda kokarin da suke nunawa a wasannin da suke shiga, tare da tabbatar da cewa kungiyar za ta kare kambunta da ikon Allah.
Shi ma shugaban kungiyar magoya bayan kungiyar Kano Pillars, Bashir Idris Mu’azu Jide ya ce Kano Pillars za ta farfado kuma za ta kasance abar misali duk da yadda ta samu kanta a yanzu. Ya ce magoya bayan kungiyar Kano Pillars sun dauki al’amarin a matsayin kalubale ga bangaren shugabannin kungiyar da masu horar da ’yan wasa.
A nasa tsokacin, mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Gwarzo, Mustapha Umar Tallo ya ce ya zamo wajibi a yaba wa ’yan wasa da shugabannin kungiyar ta Kano Pillars saboda kokarin da suke yi duk da cewa akan samu nasara a kansu. Sai dai ya yi fatan cewa masu horar da kungiyar za su kara bullo da dabarun tunkarar kalubalen da ka iya taso wa kungiyar ta yadda za ta sake komawa kan matakinta na daya.
Ya jinjina wa sabon shugaban kungiyar Alhaji Kabiru Baita saboda dawo da kungiyar mataki na 5 daga mataki na 10 a gasar, inda ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kano ta kara bai wa kungiyar kula ta musamman ta yadda za ta ci gaba da rike kambinta.