Kano ta bullo da sabon tsarin kiwon lafiya
Gwamnatin Jihar Kano ta kafa sabuwar hukumar lafiya wacce za ta tabbatar da ganin daukacin mazauna kananan hukumomin jihar 44 sun samu cin moriyar sabon tsarin kiwon lafiya a jihar. Da take jawabi a taron manema labarai da hukumar ta shirya da hadin gwiwar wasu kungiyoyi, Dokta Halima Muhammadu Mijinyawa wacce ita ce shugabar hukumar […]
Gwamnatin Jihar Kano ta kafa sabuwar hukumar lafiya wacce za ta tabbatar da ganin daukacin mazauna kananan hukumomin jihar 44 sun samu cin moriyar sabon tsarin kiwon lafiya a jihar.
Da take jawabi a taron manema labarai da hukumar ta shirya da hadin gwiwar wasu kungiyoyi, Dokta Halima Muhammadu Mijinyawa wacce ita ce shugabar hukumar ta ce tsarin ya hada da ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni da wadanda ba sa aikin gwamnati kamar masu kananan sana’o’i da mata da kuma daliban manyan makarantu.