Kano ta fara koya wa mata daukar fim da kyamara

Gwamnatin Jihar Kano ta fara horar da mata 250 sana’ar daukar hoto na kati na zamani (digital photography) da na bidiyo da kuma yadda ake tace hotuna (editing). Ta kirkiro wannan shirin ne don samar da aikin yi ga mata matasa.Mataimakiyar Daraktar Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Jihar Kano, Hajiya  Maryam Suleiman Ahmed ta ce wannan […]

Kano ta fara koya wa mata daukar fim da kyamara

Wasu daga cikin matan da Gwamnatin Kano ta koya wa daukar fim da kyamaraGwamnatin Jihar Kano ta fara horar da mata 250 sana’ar daukar hoto na kati na zamani (digital photography) da na bidiyo da kuma yadda ake tace hotuna (editing).
 Ta kirkiro wannan shirin ne don samar da aikin yi ga mata matasa.
Mataimakiyar Daraktar Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Jihar Kano, Hajiya  Maryam Suleiman Ahmed ta ce wannan shiri kirkirar wata sabuwar makaranta ce mai suna Dabo Tb Center, inda makarantar ta rubuta wa Gwamnatin Jihar Kano bukatar ta dauki nauyin mata goma daga kananan hukumomin jihar 44 don samun wannan horo, inda hakan zai ba mata damar gudanar da wannan sana’a a kananan hukumominsu.
Daga karshe gwammnati ta amince da mata biyar daga kananan hukumomin wadanda za su samu wannan horo. Bayan sun gama, gwamnatin za ta ba su jarin kama shago domin taimaka musu tsayawa da kafafunsu.
Shugabar makarantar Hajiya Fatima Dabo ta ce za su yi mako shida suna bayar da wannan horo a wannan sabuwar cibiyar bayar da horo na aikin Talabijin mai zaman kanta ta farko a Kano. An fara wannan horo ranar 16 ga watan Satumba, 2013.   Cikin horon da za su bayar har da yadda za su shirya bukukuwa na zamani baya ga aikin shirye-shiryen talabijin don tafiya da zamani.
Ta ce: “Shirin zai taimaka wajen samar da kwarraru wajen samar da masu shirin talabijin na Hausa wanda a yanzu duniya ta ke bukata.”
Malam Muhammadu Fatuhu daya daga cikin jami’an makarantar ya wannan yunkuri zai samar da aikin yi.