Kano ta kafa kwamitin da zai kula da ‘yan wasan Pillars

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani kwamitin da zai kula da ‘y an wasan kwallon kafa na Kano pillars don ganin kungiyar ta samu nasara a wasan da za a buga a gasar zakarun kulob-kulob na Afirka da aka fi sani da CAF Champions League. Aminiya ta ruwaito cewa kungiyar Kano Pillars ce za ta […]

Kano ta kafa kwamitin da zai kula da ‘yan wasan Pillars
Kano ta kafa kwamitin da zai kula da ‘yan wasan Pillars

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani kwamitin da zai kula da ‘y an wasan kwallon kafa na Kano pillars don ganin kungiyar ta samu nasara a wasan da za a buga a gasar zakarun kulob-kulob na Afirka da aka fi sani da CAF Champions League.

Aminiya ta ruwaito cewa kungiyar Kano Pillars ce za ta wakilci kasar nan a gasar da za a fara daga ranar 13 ga watan Janairun nan da muke ciki.
Da yake kaddamar da ‘yan kwamitin, mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya nemi ‘yan kwamitin da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin ‘yan wasan sun samu cikakken horo don ganin kungiyar ta samu nasara a gasar.
Dokta Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano a shirye take ta bayar da dukkanin wata gudummawa da ake bukata don kai kungiyar ta Kano Pillars ga gaci saboda a cewarsa wannnan babbar dama ce ga jihar. “zabar kungiyar Kano Pillars don wakiltar kasar nan a wannan wasa da za a yi ba karamar dama ba ce ga jihar Kano, wanda bai kamata mu yi wasa da shi ba, don haka gwamnati a shirye take ta taimakawa kungiyar don ta samu nasara. Samun nasarar kungiyar abu ne da zai kara wa jihar Kano kima ba wai kawai a Najeriya ba har ma da duniya baki daya” inji shi.
‘Yan kwamitin da aka kaddamar sun hada da shi kansa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaba da Alhaji Ibrahim Galadima da Mai ba Gwamna shawara a harkokin wasanni Alhaji Uba dan Zainab da Kwamishinan Ma’aikatar ruwa ta Jihar Dokta Yunusa dangwani da sauransu.
Da yake mayar da jawabi a madadin ‘yan kwamitin, Alhaji Ibrahim Galadima ya tabbatar wa gwamnati cewa kwamitin zai yi kokari ganin ya sauke nauyin da aka dora masa.