Kano ta Kudu: Shin Alhassan Doguwa ya ci amanar Kabiru Rurum da Kawu Sumaila?

Tafiyar ‘yan ukun ta watse tun da Ganduje ya goyi bayan takarar mataimakinsa, Nasiru Yusif Gawuna.

Kano ta Kudu: Shin Alhassan Doguwa ya ci amanar Kabiru Rurum da Kawu Sumaila?

A wani kawancen siyasa na wasu matasan ’yan siyasa da ludayinsu ke kan dawo a Kudancin Kano, inda suka dauko wani gangami wanda a tunaninsu suke ganin za su ceto al’ummar wannan yanki.

Cetowar ba ta wuce daga wariya da kuma halin ko in kula da ake nuna masu a wajen fitar da shugabanni a Jihar ba, musamman ta bangaren zartarwa wato Gwamna da Mataimakinsa.

Al’ummar da ke Jihar na sane da cewa wannan yanki ya dade yana nema a ba shi damar fitar da dan takarar da zai zama Gwamna a wannan Jihar, sai dai kash! hakan al’ummar wannan yanki ya gaza cim ma ruwa.

Yankin Kano ta kudu, a baya in muka yi duba za mu ga ya fitar da Gwamnoni har guda biyu wadanda suka mulki Kano a wannan a tsari na Dimikuradiyya, wato marigayi Alhaji Muhammad Abubakar Rimi da kuma Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, wanda a yanzu shi ne Sanata mai wakiltar wannan yanki a Majalisar Dattawa.

Sai dai tun dawowar mulkin dimokuradiyya a wannan jamhuriya ta hudu, yankin ke ta kishirwar neman ya samu ko da mataimakin Gwamnan ne amma abin ya ci tura.

A yanzu dai zamu iya cewa yau shekara 23 da dawowar wannan jamhuriya amma yankin Kudancin Kano bai amfana da komai ba sai Kakakin Majalisar Dokoki.

Bari mu dan yi duba da shugabannin da suka shugabanci Jihar Kano daga 1999 zuwa yau.

A farkon dawowar Dimokuradiyya a wannan jamhuriya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwasao, wanda ya fito daga Kano ta Tsakiya ya jagoranci Jihar har tsawon shekara hudu daga 1999 zuwa 2003 tare da Dokta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Mataimakinsa wanda ya fito daga yankin Kano ta Arewa.

Bayan hada wa’adin mulkinsa na shekara hudu sai Malam Ibrahim Shekarau, ya kayar dashi a zaben 2003, wanda daga nan ya rike Jihar har tsawon shekara takwas a jere (2003 – 2011).

Malam Ibrahim Shekarau a lokacin mulkinsa ya yi Mataimaka guda biyu, wato marigayi Injiya Magaji Abdullahi sai kuma Injiniya Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, wadanda dukkaninsu suka fito daga yankin Kano ta Arewa.

Bayan kamala wa’adinsu ne, sai Injiya Rabi’u Musa Kwankwaso ya sake dawowa a karo na biyu tare da mataikinsa na wancan lokacin, Abdullahi Umar Ganduje, inda ya karasa zango na biyu na mulkinsu.

Kazalika, bayan kammala wa’adin mulkin na Kwankwaso ya zabi mataikinsa a matsayin wanda zai gaje shi, inda ya hada takararsu da Ferfasa Hafizu Abubakar, sai dai Farfesa Hafizun bai karasa wa’adin mulkin ba bayan samun wani sabani da Gwamnan na Kano, inda ya ajiye aikin nasa.

A 2018 sai gwamna Ganduje ya zabi kwamishinansa na Harkokin Noma, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda zai maye gurbin Farfesa Hafiz, wanda da shi ne ake sa ran za su karasa wa’adin mulkin nasu tare.

Dukkanin wadannan mataimaka na Ganduje sun fito ne daga Kano ta tsakiya.

Wannan wariya da ake nuna wa wannan yanki na kudancin Kano a siyasar Jihar a wannan lokaci, shi ne ya zaburar da wasu jiga-jigai a yanki suka hada wata tafiya da suke kira da “Yan Ukun Baba Ganduje” domin su fitar da yankin daga wannan kangi na siyasa da suke ciki.

Jagorori a tafiyar sun hada da tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Kano kuma dan majalisa da ke wakiltar al’ummar Rano, Kibiya da Bunkure a Majalisar Wakilai a yanzu, Kabiru Alhassan Rurum, sai tsohon wakilin Sumaila da Takai a Majalisar Wakilai, Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila da kuma Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai kuma wakilin mazabar Tudun Wada da Doguwa, Alhasan Ado Doguwa.

Wannan tafiya dai tun kafin ta yi nisa masana da dama suka yi hasashen cewa ba inda za ta je duba da wasu dalilai, musamman idan aka yi la’akari da son zuciyar wasu daga cikin jagororin.

To amma dai za mu iya cewa tafiyar a baya ta fara armashi domin kuwa an hango jagororin a lokuta da dama suna taro domin shawo kan matsalar tasu, inda suke neman fito da daya daga cikinsu domin neman takarar gwamnan Kano a kakar zaben 2023.

Alamu sun yi nuni da cewa Kabiru Alasan Rurum, shi ne wanda za su sanya a gaba.

Sai dai kamar yadda alamu suka yi nuni, da yawa daga cikin masu fashin-bakin siyasar Kano sun tabbatar da cewa tafiyar ba za ta yi nisa ba, duba da irin mutanen da aka hada a tafiyar.

Sanin kowa ne cewa wadannan ‘yan siyasa su na da mabambantan ra’ayi sannan suna da son kansu fiye da ta al’ummarsu.

Wanda hakan ne ya sa akai hasashen cewa za su iya fifita bukatarsu a kan ta al’ummar yankin da suke wakilta, sai ga shi kuwa hakan ce ta kasance a karshen tafiyar.

Rushewar kawancen siyasar ya faru ne bayan da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya furta cewa zai goyi bayan Mataimakinsa tare da tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi a kakar zabe mai zuwa.

Wannan furuci na Gwamnan, ya sanya al’umma tunanin cewa zai harzuka dukkanin jagororin wannan tafiya, sannan su dauki matsaya guda daya tare.

Sai dai kash! an jiyo daya daga cikinsu wato, Alhasan Ado Doguwa na alakanta kansa da wannan zabi na Gwamnan.

Tuni dai aka rasa shugabanni biyu daga cikin tafiyar, domin tuni suka fice daga jam’iyyar APC a kan zargin rashin adalci daga Ganduje.

Sai dai a iya cewa Alhasan Ado Doguwa, ya makale a baya, ya zabi fifita bukatar kashin kansa a kan ta al’ummar yankin na Kano ta Kudu.

Ali Sabo dan Jarida ne kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum.

Ya rubuto daga Jihar Kano.

Za a iya tuntubarsa a kan adireshinsa na imel: [email protected]