Kano ta samu tallafin alluran riga-kafin Diphtheria 4m daga UNICEF
UNICEF ta ba wa jihohi da ke fama da cutar Diphtheria a Najeriya alluran riga-kafi guda miliyan tara
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ba wa Kano da sauran jihohi alluran riga-kafin cutar Diphtheria guda miliyan 9.3.
Daga cikin adadin da hukumar ta ba wa jihohin da aka samu bullar, UNICEF ta tura wa Jihar Kano alluran riga-kafin guda miliyan huɗu, a matsayin Kano na jihar da cutar ta fi ƙamari.
- Masana’antun Najeriya sun yi kwantan kayan N272bn a wata 6
- NAJERIYA A YAU: ‘Yadda yawan ciyo bashi zai durƙusar da Najeriya’
Wakilin UNICEF, Dokta Rownak Khan, Sauran jihohin da za su amfana da tallafin alluran riga-kafin na UNICEF su ne Bauchi, Borno, Yobe, Katsina, Kaduna da kuma Jigawa.
Hukumar ta kara da cewa nan da makonni masu zuwa za ta samu ƙarin alluran riga-kafin guda miliyan huɗu ga gwamnati domin taimaka mata wajen yaƙar cutar.
Kawo yanzu cutar Diphtheria ta hallaka mutum 453 a Najeriya kuma yawancinsu ƙananan yara ne ’yan shekaru hudu zuwa 15, waɗanda ba a taba yi musu allurar riga-kafin ba.
Mutum sama da 7,000 ne aka tabbatar suna dauke da cutar da cikin mutane sama da 11,500 da ake zargin su da alamunta.
UNICEF ta ce yara sama da miliyan biyu ne a Najeriya ba a taɓa yi wa allurar riga-kafin cutar ba, don haka ta jaddada bukatar ɗaukar duk matakan da suka dace na magance ta.