Tinubu ya nada mace minista daga Kano, Matawalle, Bagudu, Lalong sun samu shiga

Maryam Shetti da T. Gwarzo daga Kano, a yayin da Tinubu ya ba da sunan Matawalle da tsoffin gwamnoni hudu

Tinubu ya nada mace minista daga Kano, Matawalle, Bagudu, Lalong sun samu shiga

Maryam Shetty

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabi Maryam Shetty da kuma Abdullahi Tijjani Gwarzo  a matsayin ministocinsa daga Jihar Kano.

Da haka Kano ta shiga sahun jihohin da Tinubu zai nada mata ministoci da kuma wadanda suka samu ministoci biyu-biyu.

Tinubu ya kuma zabi tsohon gwamnan Zamafara, Bello Mohammed Matawalle da takwarorinsa hudu na jihohin Kebbi, Filato, Osun da Yobe, a matsayin ministocinsa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da haka yayin karanta sunayen ragowar ministoci 19 da Tinubu ya aike wa majalisar a ranar Laraba.

Ga cikakken jerin sabbin wadanda shugaban kasan ke son nadawa minista su ne:

  1. Bello Matawalle – Zamfara
  2. Abdullahi Tijjani Gwarzo – Kano
  3. Atiku Bagudu – Kebbi
  4. Ibrahim Geidam – Yobe
  5. Simon Lalong – Filato
  6. Adegboyega Oyetola – Osun
  7. Bosun Tijani – Ogun
  8. Dr Maryam Shetty -Kano
  9. Isiak Salako – Ogun
  10. Tunji Alausa – Legas
  11. Dr Yusuf Tanko Sununu – Kebbi
  12. Lola Ade John – Legas
  13. Shuaibu Abubakar Audu – Kogi
  14. Farfesa Tahir Mamman – Adamawa
  15. Sanata Aliyu Sabi Abdullahi – Neja
  16. Sanata Alkali Ahmed Saidu – Gombe
  17. Sanata Heineken Lokpobori – Bayelsa
  18. Uba Maigari Ahmadu – Taraba
  19. Zaphaniah Bitrus Jisalo – Birnin Tarayya; dan asalin Birnin Tarayya na farko da zai zama minista.

Alkaluman ministocin Tinubu

Kawo yanzu mutum 47 ne Tinubu ya mika wa majalisar domin tantancewa, inda a ranar Laraba ta kammala tantance mutum 28 na farko.

Ministoci mafiya yawa:

Da haka, Tinubu zai zama shugaban kasa da ministocinsa suka fi yawa a Najeriya a Jamhuriya ta hudu. Kafin yanzu, magabancinsa, Muhammadu Buhari, ne ya fi yawan ministoci, inda yake da 43.

Jihohi masu ministoci 2:

  1. Kano
  2. Katsina
  3. Kebbi
  4. Legas
  5. Ogun
  6. Kuros Riba

Tsoffin gwamnoni:

  1. Nasir El-Rufai – Kaduna
  2. Badaru Abubakar – Jigagwa
  3. Atiku Bagudu – Kebbi
  4. Bello Matawalle – Zamfara
  5. Ibrahim Geidam – Yobe
  6. Simon Lalong – Filato
  7. Nyesom Wike – Ribas
  8. Dave Umahi – Ebonyi
  9. Adegboyega Oyetola – Osun

Mata ministocin Tinubu:

  1. Maryam Shetty – Kano
  2. Hannatu Musawa – Katsina
  3. Iman Suleiman Ibrahim – Nasarawa
  4. Betta Chimaobim Edu – Kuros Riba
  5. Doris Uzoka Anite – Imo
  6. Stella Okotete – Edo
  7. Nkiru Onyejeocha – Abia
  8. Uju Kennedy-Ohanenye – Anambra
  9. Lola Ade John – Legas

’Yan majalisa masu ci 3:

  1. Dave Umahi
  2. Nkeriuka Onyejeocha
  3. Olubunmi Tunji-Ojo

Hadiman shugaban kasa:

  1. Hannatu Musawa
  2. Dele Alake
  3. Wale Edun.

Tsoffin ’yan majalisa:

  1. Abubakar Momoh
  2. Yusuf Tuggar
  3. Ekperipe Ekpo
  4. Abubakar Kyari
  5. John Enoh
  6. Sani Danladi
  7. Aliyu Sabi Abdullahi
  8. Alkali Ahmed Saidu
  9. Heineken Lokpobori
  10. Zaphaniah Bitrus Jisalo
Kawo yanzu dai bai ayyana ma’aikatun da zai ba wa mutanen ba, a yayin da ake jiran majalisa ta tantance mutum 19 da ya mika sunayen nasu a ranar Laraba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos