Kano ta samu rarar kudi saboda soke bada kujerun Hajji

A nata bangaren, Hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Kano ta ce soke bada kujerun hajji kyauta ya sa ta samu rarar kudi kimanin Naira biliyan 1.5, idan aka yi la’akari da kudin da ake kashewa a baya. Baban sakataren hukumar, Malam Abba Yakubu ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a […]

Kano ta samu rarar kudi saboda soke bada kujerun Hajji

A nata bangaren, Hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Kano ta ce soke bada kujerun hajji kyauta ya sa ta samu rarar kudi kimanin Naira biliyan 1.5, idan aka yi la’akari da kudin da ake kashewa a baya.
Baban sakataren hukumar, Malam Abba Yakubu ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a waya.
Ya ce Gwamntocin da suka gabata har da ta Rabi’u Musa Kwankwason wanda ya soke shirin, sun dinga bada kujeru ne da manufa mai kyau, amma daga baya da aka ga ana samun matsala, musamman na tabarbarewar arzikin kasa, tasa aka soke shirin.
Wani dalilin kuma shi ne, karin yawan al’umma, misali idan gwamnati tana daukar nauyin mutum goma a shekaru ashirin da suka wuce, yanzu sai dai ta dauki mutane dari. Sannan kuma an gano cewa mutane da yawa idan an ba su ba sa amfani da kujerar sai dai su sayar su karbi kudin su yi sha’anin gabansu.  
‘Ya kara da cewa a halin yanzu wadanda kawai gwamnati take daukar nauyi su ne wadanda za su taimaka wa alhazai kai tsaye, wadanda suka hada da “likitoci da Hisbah da Kotun tafi-da-gidanka domin shari’a ko da za a sami sabani a tsakanin alhazai. Sannan kuma gwamnati tana bada tallafi don kama gidan da alhazai za su zauna da kuma ciyar da su a Makka da Madina. ‘Duk wadanan da na lissafa maka da ma ana yinsu,  sai dai ciyarwa ce kawai da aka shigo da ita a shekarun nan. Saboda haka wannan rarar ta naira biliyan  1.5 an same ta kuma ta taimaka wajen wasu daga ayyukan raya kasa. wani lokaci kuma wasu idan an ba su ba sa tafiya sai su boye su dinga sayarwa da tsada.”