Kano ta Tsakiya: Laila Buhari ce ’yar takarar PDP —Kotu
Kotun Daukaka Kara ta soke takarar Danburam Nuhu da Jam’iyyar PDP ta gabatar a kujerar Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya
Kotun Daukaka Kara a Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Itan Mbaba ta soke takarar Danburam Nuhu da Jam’iyyar PDP ta gabatar a kujerar Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya.
Kotun ta amince da zaben fidda-gwani da jam’iyyar ta gudanar, karkashin shugabancin Shehu Sagagi, wanda ya fitar da Laila Buhari a matsayin ’yar takarar.
- Gwamnati za ta lalata bindigogi 3,000 da ta kwato a hannun ’yan ta’adda
- Bakin haure 50,000 sun mutu a hanyar neman ingantacciyar rayuwa —IOM
Haka kuma kotun ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC ) da ta soke sunan Damburam Nuhu tare da maye gurbinsa da na Laila Buhari a matsayin ’yar takarar Kano ta Tsakiya a PDP.
A anar 26 ga watan Satumba ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yi watsi da karar saboda rashin hurumin shari’a, bisa hujjar cewa an shigar da karar ne a Kano maimakon Abuja, sabanin tsarin Majalisar Shari’a ta Kasa (NJC) kan al’amuran da suka shafi kararraki kafin zabe.
Amma a hukuncin da Mai Shari’a Itang Mbaba ya yanke a ranar Laraba, Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da hukuncin da nabbar kotun, wanda ta ce kuskure ne yin watsi da karar a kan wannan batu.