Kano: ’Yan majalisar APC sun yi mubaya’a ga Aminu Ado Bayero

‘Yan majalisar sun kai ziyarar ne don adawa da matakin gwamnatin jihar na rushe masarautun Kano.

Kano: ’Yan majalisar APC sun yi mubaya’a ga Aminu Ado Bayero

Wasu daga cikin ’Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano daga tsagin jam’iyyar APC, sun kai ziyarar goyon baya ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

’Yan majalisar dai sun ziyarci Sarkin ne, a ƙaramar fadar Nassarawa da ke kan titin zuwa gidan gwamnatin Jihar Kano.

Da yake gabatar da jawabinsa, shugaban tawagar ‘yan majalisar wanda kuma shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar, Labaran Abdul Madari, ya ce sun kai wa Sarkin ziyarar ne, domin jaddada goyon bayansu a gare shi kan dambaruwar masarautar Kano.

“Dukkaninmu nan da kake gani mai martaba muna tabbatar da goyon bayanmu a gare k, kuma kai za mu ci gaba da yi wa biyayya saboda doka cewa ta yi kai ne Sarkin Kano,” a cewar Madari.

Kazalika, ya ce a madadin ‘yan uwansa suna yi wa Sarkin fatan tabbatuwar kujerarsa ta Sarkin jihar.

Da yake jawabi, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya nuna godiyarsa da ziyarar tasu, inda ya buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da addu’ar samun zaman lafiya a Kano da Najeriya baki ɗaya.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume