Kano: ’Yan sanda sun kori ’yan tauri daga Fadar Sarki

’Yan taurin da ke tsaron Sarki Muhammadu Sanusi II a fadar Gidan Rumfar sun janye a sakamakon samame da kwace ikon fadar da ’yan sanda suka yi

Kano: ’Yan sanda sun kori ’yan tauri daga Fadar Sarki

’Yan sanda sun kai samame a Fadar Sarkin Kano ta Gidan Rumfa inda Sarki Muhammadu Sanusi II yake, suka fatattaki ’yan taurin da ke gadin sa.

Mazauna unguwar sun ce a sakamakon haka, ’yan taurin suka janye daga babbar fadar a ranar Lahadi, kamar yadda kafar labarai ta Premium Times ta ruwaito.

Wani mazaunin yankin ya ce “A cikin fadar wasu ’yan taurin suka bar makamansu suka bad-da-kama suka tafi bayan an umarce su su fice daga fadar ko su yaba wa aya zalunta,” a cewar kafar.

Ta kuma ruwaito wani dan sanda daga fadar yana cewa ’yan taurin “duk sun san inda dare ya yi musu. Ko ba a fada ba, kun san yanzu ba sa nan.”

Ana iya tuna cewa ’yan tauri daga sassan jihar sun yi dafifi domin tsaron Sarki Muhammadu Sanusi II a Gidan Rumfa a yayin da ake tsaka da takaddama kan Sarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da kuma Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero.

An gayyato ’yan taurin ne a yayin da ake zargin Gwamnatin Tarayya na yunkurin dawo da Sarki Aminu Ado Bayero fadar bayan an maye gurbinsa da Sanusi II.

Sai dai kuma a halin yanzu ’yan sanda sun karbe ikon tsaron fadar Gidan Rumfa bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya mai cike da rudani kan nadin Sanusi II.

Har yanzu dai ana ta takaddama game da hukuncin da Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya yanke da ake cewa ta soke nadin Sanusi II.

Hakan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da wasu majiyoyi ke rade-radin cewa Gwamnatin Tarayya na shirin dawo da Aminu Ado Bayero Fadar Gidan Rumfa daga karamar Fadar Nassarawa da yake.

Tun dawowarsa Kano a watan Mayu Aminu Ado Bayero da kariyar jami’an tsaro ya tare a Fadar Nassarawa sakamakon sauke shi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, ya maye gurbinsa da Sanusi II.

A yayin da yake zaune a Fadar Nassarawa, Aminu Ado Bayero, ya samu tsaro daga sojoji da ’yan sanda da kuma jami’an Sibil Difens.

Ana iya tuna cewa a makon jiya Gwamnatin Kano ta ba da umarnin fitar da shi da kuma rushe Fadar Nassarawa ta kuma aike da motocin aiki da cewa za a fara aikin gyaran karamar fadar.

Lamarin dai ya haifar da zullumi.

A ranar Juma’a kuma Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da haramta ayyukan ’yan tauri da ’yan banga a fadin jihar.

A hukuncin da mai Shari’a Abdullahi Liman ya yanke hukunci, ya haramta aiwatar da sabuwar dokar Masautun Jihar Kano da ta nada Sarki Muhammadu Sanusi II sakamakon sauke masarautun jihar guda biyar.

Alkalain ya ba da umarnin ne kan abin da ya ce gwamnatin jihar ta yi na kin umarnin kotu na dakatar da yin sabuwar dokar masarautun.

Sai dai kuma ya bayyana cewa gwamantin jihar na da hurimin yin sabuwar dokar tare da ba da umarnin komai ya tsaya a inda yake.

Da hakan bangaren gwamnati ke ikirarin samun nasara da kuma samun amincewar kotun.

Har yanzu dai lauyoyi na ta muhawara kan wannan hukunci.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda