Kano za ta samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta – Ganduje
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta hada kai da kasar Spain don samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta don farfado da masana’antu a jihar.Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin sabbin zababbun Shugbannin Cibiyar Ciniki, Ma’adinai da Al’amuran Noma ta Jihar Kano (KACCIMA) […]
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta hada kai da kasar Spain don samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta don farfado da masana’antu a jihar.
Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin sabbin zababbun Shugbannin Cibiyar Ciniki, Ma’adinai da Al’amuran Noma ta Jihar Kano (KACCIMA) a gidan gwamnati.
Gwamnan ya bayyana cewa rashin tsayayyiyar wutar lantarki shi ne makasudin da ya jawo durkushewar masana’antu a jihar. “Sanin kowa ne sai da wutar lantarki harkokin kasuwanci, musamamn ma na masana’antu ke tafiya. Lamarin da ya jawo kusan dukkanin masana’antunmu suka durkushe a halin yanzu, babu shakka hakan ba karamin ci baya ba ne a harkar kasuwanci,” inji shi.
Ganduje ya hori shugabannin na KACCIMA da su yi kokari wajen ganin jihar ta ci gaba da rike kambunta na cibiyar kasuwanci.
A nasa jawabin sabon zababben Shugaban KACCIMA Alhaji Umar Faruk dansuleka ya bayyana cewa za su yi kokarin dora kasuwannin jihar a bisa tsarin da zai ciyar da harkar kasuwanci gaba. “muna sane da yadda harkar kasuwanci ta tabarbare a jihar nan, hakan ya sa muke so mu dora kasuwanninmu a kan wani tsari da zai ciyar da harkar kasuwanci gaba wanda kuma zai zama ya yi daidai da yadda ake tafiyar da harkar kasuwanci a duniya,” inji shi.
A karshe shugaban ya yi kira ga sauran ’yan kasuwa da su bai wa cibiyarsu hadin kai don kai wa ga gaci.