‘Kanshi’

Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari ne a kan ‘kanshi’. Labarin ya yi nuni da yadda kanshi na daya daga cikin abin da ake so. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi An yi wani attajirin mai kudi a wani kauye. Attajirin […]

‘Kanshi’

Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari ne a kan ‘kanshi’. Labarin ya yi nuni da yadda kanshi na daya daga cikin abin da ake so. A sha karatu lafiya.

Taku; Amina Abdullahi

An yi wani attajirin mai kudi a wani kauye. Attajirin ya kasance yana da kirki domin yana taimakawa talakawa. Ga shi babu abin da ba shi da shi na wadata, sai dai kash! dansa ba yi da wasu abokai sai abokan banza.

Wannan hali na dansa na bata masa rai domin dan ya kasance ba ya jin maganarsa sai abin da ya ga dama yake yi har yakan fada wa mahaifinsa ya daina yi masa fada.

Rannan sai wani babban malami ya shigo gari. Mutanen garin na ganin girman malamin sosai, sai attajirin ya ziyarci  malamin ya fada masa matsalolin da yake fama da shi. Sai malamin ya aika a kirawo masa yaron.

Yaron na isowa gidan malamin, sai ya umarce shi ya tsinko masa fulawa mai kanshi. Sai yace ya ajiye fulawar a kusa da buhun dawa. Bayan awa daya ya ce da shi ya shinshina ko da sauran kanshi a jikin fulawar, yaro ya ce akwai. 

Malam ya sake cewa ya  ajiye fulawar a kusa da buhun kashin dabbobi. Bayan awa daya sai yace ya dauko. Yaro ya sake shinshinawa amma kanshin bai canza ba. Sai malamin ya ce haka yake so ya zama kamar kanshin fulawa duk inda ka shiga za a rika yaba maka.

Tun daga ranar yaron ya zama mutumin kirki, ya daina bin abokan banza.