kanshin miya ya jawo wa mai abincin gwangwani tuhuma

Wani mai sarrafa miya da abincin gwangwani day a shahara da miyar Sriracha zai fuskanci hukuncin shari’a, bisa tuhumar gurbata iskar da mutane ke shaka a kusa da masana’antars ad ake Kudancin Jihar Kalifoniya ta kasar Amurka.Jami’an hukuma a birnin Irwindale sun kai kara a Babar Kotun Los Angele a ranar Litinin din da ta […]

kanshin miya ya jawo wa mai abincin gwangwani tuhuma

Sriracha sauce from Huy Fong Foods on sale during the grand opening of a Wal-Mart Stores Inc. location in the Chinatown neighborhood of Los Angeles, California, U.S., on Thursday, Sept. 19, 2013. Photographer: Patrick T. Fallon/Bloomberg

Wani mai sarrafa miya da abincin gwangwani day a shahara da miyar Sriracha zai fuskanci hukuncin shari’a, bisa tuhumar gurbata iskar da mutane ke shaka a kusa da masana’antars ad ake Kudancin Jihar Kalifoniya ta kasar Amurka.
Jami’an hukuma a birnin Irwindale sun kai kara a Babar Kotun Los Angele a ranar Litinin din da ta gabata, inda suka bukaci a dakatar da sarrafa abincin gwangwani a masana’antar Huy Fong Foods; sun yi ikrarin cewa zafin girkijn attarugu da ke fita daga masana’antar yana cutar da al’umma.
Jami’an birnin, sun bayyana cewa, mazaunan birnin sun koka kan zafin yaji a idanunsu da makogwaro da ciwon kai, wasu ma sun ce wannan yanayi ya tursasu barin gidajensu don su tsira daga kamshin miyar.
Wasu iyalai da ke gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwa, dole suka koma cikin dakunansu, domin karfin yajin da ke bugawa a kamshin miyar ya hana a gudanar da bikin, kamar yadda Lauyan Hukumar Birnin Irwindale, Fred Galante ya bayyana wa jaridar Los Angeles Times.

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda