KANSIEC ta rage kuɗin takarar zaɓen ƙananan hukumomin Kano

KANSIEC ta tsayar da 26 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Kano.

KANSIEC ta rage kuɗin takarar zaɓen ƙananan hukumomin Kano

Shugaban KANSIEC;, Farfesa Sani Lawal Malumfashi

Hukumar Zaben Jihar Kano (KANSIEC), ta rage kudin fom din tsaya wa takara a zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe.

Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya sanar da hakan a taron masu ruwa da tsaki dangane da zaben ƙananan hukumomin jihar da za a yi a watan Oktoba.

Farfesa Malumfashi ya ce an yi ragin ne biyo bayan umarnin kotu ta da buƙaci a sake nazari kan kudin sayen fom ɗin tsayawa takara.

A cewarsa, a yanzu KANSIEC ta amince mai neman kujerar shugaban karamar hukuma ya biya naira miliyan tara.

Haka kuma, Farfesa Malumfashi ya bayyana cewa masu neman kujerun kansiloli za su sayi fom dinsu a kan naira miliyan hudu.

Wannan na nufin hukumar zaben ta amince da rage naira Miliyan guda kan farashin da ta sanya a baya, lamarin da Farfesa Malumfashi ya ce an mutunta umarnin kotu.

Ana iya tuna cewa, a bayan nan ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da sayar wa ’yan takara fom ɗin shiga zaɓen ƙananan hukumomin Kano.

Kotun ta miƙa wannan umarni ne ga Hukumar KANSIEC wadda ta ƙayyade farashin naira miliyan 10 ga masu neman shiga zaɓen kujerar shugaban karamar hukuma da kuma naira miliyan biyar ga masu neman shiga takarar kujerar kansila.

Aminiya ta ruwaito cewa, wasu jami’yyun siyasa da suka haɗa da APP da ADP da SDP ne suka yi ƙarar Hukumar ta KAINSEC a gaban kotun kan abin da suka kira tsawwala farashin fom ɗin takara domin hana su shiga zaɓen.

Hukumar KANSIEC dai ta tsayar da 26 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin a Jihar Kano a maimakon 30 ga Nuwamba da ta sanya da farko.

DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a?

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Tags