Kanti Bello: Najeriya ta rasa dan kishin kasa – Buhari da Saraki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara suna daga cikin dimbin jama’ar da suka yi ta’aziyyar rasuwar Sanata Muhammadu Kanti Bello wanda Allah Ya yi wa rasuwa a daren Talatar da ta gabata a gidansa da ke Abjua. Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyya ga […]

Kanti Bello: Najeriya ta rasa dan kishin kasa – Buhari da Saraki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara suna daga cikin dimbin jama’ar da suka yi ta’aziyyar rasuwar Sanata Muhammadu Kanti Bello wanda Allah Ya yi wa rasuwa a daren Talatar da ta gabata a gidansa da ke Abjua.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyya ga iyalai da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Katsina kan rasuwar dan siyasar. 

Wata sanarwa da Kakakinsa Femi Adesina ya fitar ta ce, Shugaban kasar kuma ya mika ta’aziyya ga Majalisar Dattawa kan wannan rashi.

Sanarwar ta ce, “A matsayinsa na Sanatan yankin Daura a shekarar 2003 da 2011, Buhari ya tuno cewa yana fitowa ya yi magana sosai kuma mutum ne mai kishin kasa da karfin hali wanda kuma ya yi aiki bil hakki da gaskiya don tabbatar da dukan matakan gwamnati a kasar nan sun sauke nauyin da ke kansu kuma su tsare aikin da ke kansu. Shugaba Buhari ya bukaci iyalan Kanti Bello da ’yan uwa da abokansa su girmama shi ta hanyar ci gaba da dabbaka halayensa na gaskiya da rikon amana, wadanda ya yi fice a kansu a daukacin lokacin da yake aiki. Kuma ya roki Allah Ya bai wa iyalan hakurin jure wannan rashi kuma Ya gafarta masa.”

A nasa sakon ta’aziyyar Dokta Bukola Saraki, ya nuna kaduwarsa ne kan rasuwar Sanata Kanti Bello.

Wata sanarwa da Kakakinsa Yusuph Olaniyonu ya fitar ta ce, Sanata Saraki ya bayyana marigayi Kanti Bello da dan majalisa mai karsashi da karfin hali da a kullum bukatun kasa suke yi masa jagoranci a yayin gudanar da ayyukansa na majalisa.

 “Rasuwar Sanata Kanti Bello, ta sa Majalisar Dattawa da Majalisar Dokoki ta kasa sun rasa mashawarcin da ake dogara da shi, wanda shugabanni da daidaikun ’yan majalisar ke neman shawarwarinsa kan al’amuran da suka shafi kasa a koyaushe,” inji Saraki.

Ya kara da cewa: “Lokacin da yake Majalisar Dattawa, marigayi Kanti Bello ya yi fice wajen bayyana ra’ayinsa kuma mutum ne mai hangen nesa da karfin hali wajen fadin gaskiya ga wadanda suke mulki ba tare da lura da jam’iyyar da suka fito ko addininsu ko kabilarsu.”

A nasa sakon ta’aziyyar Barista Yakubu Dogara, ya ce “Alhaji Kanti Bello dan siyasa ne da ya ginu tun daga tushe kuma ya bauta wa kasar nan yadda ya kamata a mukamai daban-daban, ciki har da Majalisar Dattawa. Kuma ya bar abin misali na kishin kasa da sadaukar da kai.”

Sanarwar da Kakakinsa Turaki Hassan ya fitar ta ruwaito Dogara yana kara cewa: “Ina mika sakon ta’aziyya ga iyalai da jama’a da gwamnatin Jihar Katsina da kuma daukacin kasar nan kan wannan babban rashi.”

A sakon ta’aziyyarsa Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana Sanata Kanti Bello da cikakken dan kishin kasa wanda yake matukar kaunar Najeriya da jiharsa ta Katsina ta yadda a koyaushe yake shirye ya yi hidima a kowane mataki.

Kakakin Masari, Abdu Labaran ya ruwaito Gwamna Masari yana cewa: “Rasuwar Bello a wannan lokaci na kalubale ya sa kasar nan ta rasa daya daga cikin fitattun ’yan siyasarta masu fada-a-ji.”

Sanata Kanti Bello, mai shekara 72 jigo ne a Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan, kuma ya taba zama Manajan Daraktan Kamfanin karafa na Katsina kafin ya shiga harkar siyasa inda ya zama Sanatan yankin Daura sau biyu.