Kanu Nwankwo ya zama shugaban Enyimba
Tsohon ɗan wasan Super Eagles ta Najeriya da Arsenal ta Ingila, Kanu Nwankwo ya zama shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enyimba dake Aba. Gwamnan jihar Abia Alex Otti ne ya naɗa shi wannan shugabanci kamar yadda kakakinsa Kazie Uko ya sanar. Kanu ya maye gurbin Felix Anyansi-Agwu wanda ya shugabanci ƙungiyar tsawon shekaru 24. Ban […]
Tsohon ɗan wasan Super Eagles ta Najeriya da Arsenal ta Ingila, Kanu Nwankwo ya zama shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enyimba dake Aba.
Gwamnan jihar Abia Alex Otti ne ya naɗa shi wannan shugabanci kamar yadda kakakinsa Kazie Uko ya sanar.
Kanu ya maye gurbin Felix Anyansi-Agwu wanda ya shugabanci ƙungiyar tsawon shekaru 24.
Ban ji dadin yadda gwamnati ke yunkurin kwace mini Otel ba – Nwanko Kanu
Kanu ya shawarci Ighalo ya ci gaba da yi wa Eagles kwallo
A zamanin Anyansi-Agwu, Enyimba ta ɗauki kofin zakarun Afirka har sau biyu da kuma kofin gasar firimiyar Najeriya sau tara.
A yanzu haka dai, tsohon takwaran Kanu a Super Eagles da Ajax ta Amsterdam, Finidi George ne kocin ƙunigyar.
Kuma shi ya jagoranci Enyimba ta samu nasarar cin kofin ƙwallon ƙafa na Najeriya a karo na tara tare da samun gurbin shiga gasar ƙofin nahiyar Afirka a baɗi.