Kanu ya shawarci Ighalo ya ci gaba da yi wa Eagles kwallo
Tsohon dan kwallon kulob din Arsenal da Super Eagles, Nwankwo Kanu a ranar ya shawarci dan kwallon Manchester United Odion Ighalo ya canja shawarar daina yi wa Eagles kwallo. Kanu ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da kafar labarai ta Naijanews.com a ranar Litini inda ya shawarci Ighalo da yanzu ke wasa […]
Tsohon dan kwallon kulob din Arsenal da Super Eagles, Nwankwo Kanu a ranar ya shawarci dan kwallon Manchester United Odion Ighalo ya canja shawarar daina yi wa Eagles kwallo.
Kanu ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da kafar labarai ta Naijanews.com a ranar Litini inda ya shawarci Ighalo da yanzu ke wasa a kulob din Manchester United na Ingila ya canja hukuncin da ya yanke na daina yi wa Eagles kwallo a bara.
Oddion Ighalo dan shekara 30 ya daina yi wa Eagles kwallo ne jim kadan bayan an kammala gasar cin Kofin Afirka a Masar inda Najeriya ta zama ta uku kuma ya zama dan kwallon da ya fi yawan zura kwallo a raga da kwallo 6 a gasar.
Shi dai Ighalo yana wasa ne a kulob din Shenghai Shenhua da ke China amma ya koma Man United a watan Janairun bana a matsayin aro na tsawon wata shida. Kawo yanzu ya zura kwallo uku a raga a dukkan wasannin da ya yi a United da hakan ya nuna tauraruwarsa na haskakawa.