Kanu ya yaba wa dan kwallon Fyling Eagles Taiwo Awoniyi

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Nwankwo Kanu ya yaba wa dan kwallon Fyling Eagles Taiwo Awoniyi a bisa haskakawar da yake yi a halin yanzu. Kanu ya ce idan dan kwallon ya daure da haka, zai samu daukaka a fagen kwallon kafa a duniya.dan kimanin shekara 18, Taiwo Awoniyi dai yana […]

Kanu ya yaba wa dan kwallon Fyling Eagles Taiwo Awoniyi
Kanu ya yaba wa dan kwallon Fyling Eagles Taiwo Awoniyi

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Nwankwo Kanu ya yaba wa dan kwallon Fyling Eagles Taiwo Awoniyi a bisa haskakawar da yake yi a halin yanzu.

Kanu ya ce idan dan kwallon ya daure da haka, zai samu daukaka a fagen kwallon kafa a duniya.
dan kimanin shekara 18, Taiwo Awoniyi dai yana haskakawa a ’yan kwanakin nan a kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20) inda ya taimaka wa kungiyar lashe kofin matasa na Afirka na shekarar 2015 sannan shi ya zura kwallaye biyun da suka sanya Flying Eagles hayewa gasar wasanni ta Afirka (All Afircan Games).
Kamar yadda Kanu da ake wa lakabi da Papilo ya sanar a shafin sadarwarsa na Twitter ya ce “idan Awoniyi ya daure da haka, ko shakka babu zai yi suna a fagen kwallon kafa a duniya da hakan zai sa ya samu daukaka”.