Kanu ya zama na 13 a tarihin ’yan kwallon Arsenal

Tsohon dan kwallon Najeriya da ya yi wa kulob din Arsenal na Ingila kwallo a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2004 Nwanko Kanu ya kasance na 13 a jerin ’yan kwallon da suka fi nuna kwazo a kulob din tun daga kafuwarsa kawo yanzu. Bayanin haka na kunshe ne a wata kuri’a da magoya bayan kulob […]

Kanu ya zama na 13 a tarihin ’yan kwallon Arsenal
Kanu ya zama na 13 a tarihin ’yan kwallon Arsenal

Tsohon dan kwallon Najeriya da ya yi wa kulob din Arsenal na Ingila kwallo a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2004 Nwanko Kanu ya kasance na 13 a jerin ’yan kwallon da suka fi nuna kwazo a kulob din tun daga kafuwarsa kawo yanzu.

Bayanin haka na kunshe ne a wata kuri’a da magoya bayan kulob din da ke Ingila suka jefa a yanar sadarwar kulob din inda suka zabo ’yan kwallo 50 da suka fi yin fice a kulob din tun daga kafurwarsa kawo yanzu.
Kanu dai ya yi wa kulob din Arsenal wasanni 198 kuma ya samu nasarar zura kwallaye 48. Ya samu nasarar lashe kofin FA da na Firimiya a lokacin da ya yi wasa a kulob din.
Theirry Henry ne aka zaba a matsayin na farko sai na biyu aka zabi Dennis Bergkamp yayin da aka zabi Ray Parlour a matsayin na 19.
Ga kadan daga cikin jadawalin ’yan kwallon kulob din Arsenal da magoya bayan suka zaba kamar haka:
1. Thierry Henry
2. Dennis Bergkamp
3. Tony Adams
4. Ian Wright
5. Patrick bieira
6. Robert Pires
7. Dabid Seaman
8. Liam Brady
9. Charlie George
10. Pat Jennings
11. Freddie Ljungberg
12. Marc Obermars
13.Kanu Nwankwo
14. Dabid O’Leary
15. Sol Campbell
16. Dabid Rocastle
17. Pat Rice
18. Cliff Bastin
19. Ray Parlour
20. Martin Keown