Kanye West da Kim Kardashian sun yi baiko
A ranar Litinin da ta gabata ce fitaccen mawakin zamanin nan, Kanye West da shahararrar mai shirya wasannin talabijin, Kin Kardashian suka yi baiko, bayan sun share sama da shekara daya cur suna soyayya, soyayyar da ta samar masu da haihuwar yarinya.’Yan wasan biyu, sun yi baikon ne a daidai ranar da aka yi bikin […]

A ranar Litinin da ta gabata ce fitaccen mawakin zamanin nan, Kanye West da shahararrar mai shirya wasannin talabijin, Kin Kardashian suka yi baiko, bayan sun share sama da shekara daya cur suna soyayya, soyayyar da ta samar masu da haihuwar yarinya.
’Yan wasan biyu, sun yi baikon ne a daidai ranar da aka yi bikin cikar ita Kim Kardashian shekara 33 da haihuwa. A ranar ce shi Kanye, a gaban abokai da ’yan uwa, ya sanya wa matar tasa zoben alkawari, sannan makada da mawaka suka cashe a dandalin AT & T Park da ke birnin San Francisco na kasar Amurka.
Ko wane dalili ya sanya ya zabi wannan rana domin baikon nasu? Kanye West ya ce: “Ina so ne karrama ta a wannan rana ta zagayowar haihuwarta, domin kada ta mance da ita har abada a rayuwarta. Ta samu kyakkyawan wurin zama, tana da diya mai lafiya, sannan ita kuma tana cikin murna da lafiya, don haka ga shi kuma yanzu mun yi baiko, shi ne tambarin da ya cikasa mata farin cikinta na rayuwa.”
Nan gaba kuma ake sa ran za su fitar da lokacin da za a yi bikin auren nasu, kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.