Karɓa-karɓa: Ban taɓa ƙulla yarjejeniya da Atiku ba —Kwankwaso
Kwankwaso ya ce bai san daga inda magoya bayan Atiku suka ƙorƙiro labarin da suke yaɗawa ba
Tsohon Gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP a zaɓen 2013, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ƙaryata labarin da ke cewa ya ƙulla yarjejeniyar karɓa-karɓar mulki da sauran ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun adawa —Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na LP.
A hirar da BBC Hausa ta yi da shi, Kwankwaso ya ce bai san daga inda aka ƙirƙiro maganar ba. Amma ya yi iƙirarin samun labari cewa ɓangaren Atiku suna tattaunawa da shugabanni a shiyyoyin siyasar Najeriya, da malaman addini, suna tallata musu ƙagaggen labarin.
Kwankwaso ya ce “Raina ya matuƙar ɓaci da na ji shugabanni masu kima suna yada ƙarya a kan abin da bai faru ba. Na samun labarin cewa an tara malaman addini kusan 45 aka faɗa musu wannan labarin ƙanzon kurege. Ban ji daɗi ba ko kaɗan,” in ji Kwankwaso.
Ya ci gaba da cewa, “an shaida wa malaman cewa, wai ni da Atiku mun ƙulla yarjejeniya cewa zai yi mulkin shekara huɗu daga nan sai ni ma in yi shekara huɗu, sannan Peter Obi ya yi shekara takwas. Wannan karya ce tsagwaronta, domin babu inda muka taba ƙulla wannan yarjejeniya,” in ji Sanata Kwankwaso.
- A biya mutanen da jirgin soji ya kai wa hari a Sakkwato diyya —PDP
- Sojojin Faransa: Dalilin da Janar Tchiani ya zargi Najeriya
Ya bayyana cewa tun da ya bar PDP ya dawo NNPP ya samu kwanciyar hankali, ya kuma nisanci abin da ya kira, ƙunyatawar da ake masa da magoya bayansa a PDP.
“Irin waɗannan ƙarairayi da yaudara na daga cikin abubuwan da suka sa ni da Peter Obi da Wike da wasu muka bar PDP, yanzu kuma sun dawo suna neman mu mu taimaka wa waɗanda suka wulaƙanta mu domin biyan buƙatunsu.”