‘Kar ECOWAS ta kara rura wutar rikici a yankin Sahel saboda juyin mulkin Nijar’
Kar mu bari zaman lafiyar yankin Sahel ya tabarbare wajen dawo da tsarin dimokuradiyya a Nijar.
Fitaccen Malamin nan na Addinin Islama, Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo, ya ja hankalin Shugaban Bola Ahmed dangane da daukar matakin da zai kara rura wutar rikici a yankin Sahel.
Gargadin fitaccen malamin na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya shaida wa Majalisar Dokoki matsayar da kungiyar ECOWAS ta cimma kan daukar matakin soji a kan Nijar da kuma sauran takunkuman da aka dauka na ladabtar da sojojin da suka yi juyin mulki.
- Abin da ’yan Najeriya ke cewa kan janye sunan Maryam Shetty daga jerin ministoci
- DPO ya biya wa saurayi sadakin aure
Aminiya ta ruwaito, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da sakon shugaban ƙasar inda ya karanto kai tsaye daga wasikar shugaba Tinubun.
Wasikar na cewa “Bayan abin takaicin da ya faru a Nijar inda aka hambarar da shugaban kasa, ECOWAS a karkashin jagorancina ta yi Allah-wadai da juyin mulkin kuma ta amince da daukar matakan dawo da Nijar kan turbar dimokuradiyya.
“Za a rufe duk iyakokin Nijar da kasashenmu da kuma sanya ido don tabbatar da cewa an yi biyayya ga matakin.
“Yanke wutar lantarkin da ake kai wa Nijar da neman goyon bayan kasashen duniya wajen aiwatar da matsayar kungiyar ECOWAS da kuma datse sufurin jirgin sama daga cikin Nijar da ma wanda zai shiga ƙasar.
“Rufe hanyoyin shigar da kaya Nijar daga Legas da kuma wayar da kan ’yan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta game da shirin daukar matakin soji a kan sojojin Nijar din.”
Sai dai a yayin wani zaman gabatar da karatu da ya yi a ranar Alhamis da ta gabata, Sheikh Rijiyar Lemo ya ce akwai bukatar ECOWAS karkashin jagorancin Shugaba Tinubu ta sake nazari domin kuwa alakar da ke tsakanin Nijar da Najeriya ta zarce ta makwabtaka ta kai matsayin ’yan uwantaka.
A cewarsa, muddin sojoji suka kai mamaya Jamhuriyyar Nijar, to kuwa babu shakka hakan zai kara kara rura wuta a kan dimbin kalubalen zamantakewa da tattalin arziki a yankin Sahel, inda yake shawartar ECOWAS ta da ta sake tunani.
Ya ce, “Ya kamata ECOWAS ta samar da hanyoyi na lumana da za su yi wa ’yan kasar Nijar da ma yankin aiki ba tare da nuna wata kiyayya ba.
“Kowa ya san cewa yaki, musamman a wannan lokacin, yana zuwa da sakamako daban-daban.
“Ba za mu san lokaci ko kuma yadda lamarin zai kare ba. A yanzu da duniya ta kai wani munzali da kowace kasa ta kulla wata alaka da wasu kasashe masu karfi kuma Nijar na da dimbin arzikin Uranium da wadannan kasashe ke nema.
“Yanzu kusan ko’ina a yankin Sahel akwai wata kullalliyar gaba, don haka muddin wata ta tashi a Nijar, zai kara tsananta matsalar jin kai a yankin.
“Bai kamata a kokarin kashe wannan wutar a kunna wata ba, saboda muddin aka dauki matakin soji, al’ummar Nijar ne za su kwana a ciki.
“Bai kamata shugabanninmu su zama tamkar Turawa ko kuma tsoffin ’yan mulkin mallaka ne suke juya al’amuransu ba. Kar mu bari zaman lafiyarmu ya tabarbare don kawai ana son dawo da tsarin dimokuradiyya.
A bayan nan ne dai shugabannin kasashen kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma ECOWAS, suka bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar wa’adin kwana bakwai su mayar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum kan mulki.
Wannan dai shi ne matakin da kungiyar ta dauka a taron da ta gudanar ranar Lahadin makon jiya a Abuja, babban birnin Najeriya.