Kar nake ganin ka

Wani dan sanda ne ya kama kugun dan sholisho a kamen da suka je, sai ya lura akwai kudi a aljihun dan sholin. Cikin dabara sai ya zura hannu zai zaro kudin, ashe dan sholisho ya ankara, sai ya fashe da dariya yana kallon dan sanda; ya ce: “Kai barawo, kar nake ganinka dan kwana-kwana.” […]

Kar nake ganin ka
Kar nake ganin ka

Wani dan sanda ne ya kama kugun dan sholisho a kamen da suka je, sai ya lura akwai kudi a aljihun dan sholin. Cikin dabara sai ya zura hannu zai zaro kudin, ashe dan sholisho ya ankara, sai ya fashe da dariya yana kallon dan sanda; ya ce: “Kai barawo, kar nake ganinka dan kwana-kwana.” dan sanda ya ji haushi jin an ce masa dan kwana-kwana, ya zabga masa mari. dan sholi ya yi taga-taga ya dawo yana duban dan sandan sosai, ya ce: “Au sori, izi; ai ban ga igiyar ba sai yanzu.”
Daga Halima Shata Katsina (anti Dubu), 08131014066