Kara mayar da annobar rashin tsaron Jihar Zamfara siyasa ce
“Wannan shi ne karo na bakwai da muke irin wannan taro a jihar nan. Muna fata taro na gaba ya zama na murnar dawowar zaman lafiya ne a jiharmu ta Zamfara.” Wasu daga cikin kalaman Mai martaba Sarkin Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Zamfara Alhaji Attahitu Muhammad Ahmad ke nan a lokacin da […]
“Wannan shi ne karo na bakwai da muke irin wannan taro a jihar nan. Muna fata taro na gaba ya zama na murnar dawowar zaman lafiya ne a jiharmu ta Zamfara.” Wasu daga cikin kalaman Mai martaba Sarkin Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Zamfara Alhaji Attahitu Muhammad Ahmad ke nan a lokacin da aka yi taron masu ruwa-da-tsaki kan tabarbarewar tsaro a Gusau babban birnin Jihar Zamfarar a ranar Talata 9-4-19. Taron ci gaba ne da ganawa da jama’a a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan sandan kasar nan Alhaji Muhammad Adamu ke yi da niyyar tattaunawa kan yadda za a gano bakin zaren matsalolin tsaro da aikace-aikacen ’yan ta’adda masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da masu kashe-kashe da kone gidaje da dukiyoyin al’umma, baya ga satar shanu da sauran dabbobi a jihohin.
Sarkin na Anka da ya yi jawabi ne a madadin Majalisar Sakunan Jihar a gaban dukkan sarakunan jihar da wakilin Gwamnan Jihar da Ministan Tsaro Birgediya Janar Mansur Dan-Ali (mai ritaya) da jami’an tsaro da sauran masu fada-a-ji na jihar. Sarkin ya koka kan irin yadda babu ’yan sanda a dukkan karkarar jihar, wadanda kuma ake da su a hedkwatocin kananan hukumomin jihar 17, ba su wuce 150 a kowace karamar hukuma ba. Jami’an da Sarkin na Anka ya ce sun yi matukar kadan.
A tarihi inji Mai martaba Sarkin Anka rikicin ta’addacin jihar ya fara ne daga kananan barayin dabbobi, amma sannu a hankali ya rikide ya kuma bunkasa tare da yaduwa a kusan dukkan sassan jihar ya zama na aikata manyan laifuffuka na kashe-kashe da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kona gidaje da dukiyoyin al’umma.
Shi ma da yake nasa jawabin Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi wanda ya wakilci Gwamnan Jihar, Alhaji Abdul’aziz Yari, kokawa ya yi a kan irin yadda a kullum ake ta kashe-kashe da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa a jihar ta Zamfara, duk kuwa da irin jami’an tsaron da ake da su a jihar. Ya ce yanzu ta kai ’yan ta’addan suna aike wa da mutanen kauyuka sakon za su kawo musu hari, kuma hakan ta tabbata, al’amarin da ya kai fagen yanzu wadansu mutanen kauyuka suna shiga cikin ta’addancin.
A fadar Gwamna Yari mutanen da aka kashe a jihar bayan bayyanar wannan annoba sun kai dubu 3, yayin da kauyuka kusan 500, annobar tashe-tashen hankulan ta shafa.
Kusan dukkan jami’an gwamnatin jihar ta Zamfara da suka yi jawabi a wannan taro da Sufeto Janar, ba wanda ya boye bacin ransa a kan irin mawuyacin halin rashin tsaro da mutanen Jihar Zamfara suka dade suna fama da shi. Shi kansa Shugaban Karamar Hukumar Zurmi, Dokta Auwal Bawa Moriki, wanda ya ce yana jawabi ne a madadin Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Kasa (ALGON) reshen jihar, wato Shugaban Karamar Hukumar Birnin Magaji, wanda ya ce a lokacin yana can yana halartar jana’izar mutanensa 14, da ’yan ta’addar suka kashe a yankinsa, zargin sojojin da suke yaki da ’yan ta’adda a jihar ya yi kan yadda suke shakulatin bangaro a kan yaki da ’yan ta’addan.
Ya ce sojojin sun aike wa gwamnatin jihar wata takarda, wadda a ciki suke nuna kin amincewarsu da ’yan sa-kai na farar hula 8,500 da gwamnatin jihar ta dauka aiki don su rika taimaka wa sojojin. Yana mai cewa “Ko dai jami’an tsaron ba a shirye suke ba wajen kawo karshen ta’asar ’yan ta’addan ba, ko kuma ba sa son ’yan sa-kan su rika kai rahoton ayyukan ta’asar da (sojojin) suke aikatawa.” Shugaban Karamar Hukumar Zurmin ya koka kan yadda ta’asar ’yan ta’addar ta kawo mummunar koma-baya ga harkokin rayuwa da tattalin arziki da na zamantakewa a jihar.
Shi kuma Minista Tsaro Birgediya Janar Mansur Dan-Ali a sanarwar da Kakakinsa Kanar Tukur Gusau (mai ritaya) ya fitar a ranar wancan taro zargin wadansu sarakunan jihar da wadansu masu fada-a-ji a jihar da ma a Shiyyar Arewa maso Yamma ya yi da hada baki da ’yan ta’adda a shiyyar wajen ba su bayanan sirri da suke amfani da su wajen aikata ta’asa a shiyyar. Hakazalika sanarwar ta ce irin wadannan bayanan shirri da gwamnatin take da su ne ya sanya ta ba da umurnin a gaggauta rufe dukkan wuraren da ake hakar ma’adanai a Jihar Zamfara saboda an gano cewa akwai hadin baki na kut-da-kut a tsakanin masu hakar ma’adanan da ’yan ta’addan.
Zargi da Ministan Tsaron ya yi a kan sarakunan Jihar Zamfara bai yi masu dadi ba, abin da ya sa cikin fushi Majalisar Sarakunan ta mayar da martani inda take nisanta sarakunan da yin haka, sannan ta kalubalanci duk wani mai wata kwakkwarar shaida a kan wani Basarake na aikata haka, to, Gwamnatin Tarayya ta fallasa shi tare da hukunta shi kamar yadda doka ta tanada. A gefe daya kuma Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara ta zargi Rundunar Mayakan Sama da ta kai wasu hare-hare a tsakanin 8 zuwa 11 ga Afrilu a wasu yankunan jihar da take zargin maboyar ’yan ta’adda ne, hare-haren da mayakan sama suka ce sun yi nasarar kashewa tare da tarwatsa ’yan ta’adda a dazuzzuka Rugu da Sububu da Kagara, sarakunan sun yi zargin a kan faren hula ya kare.
Mai karatu idan kana biye da wannan sabarta-juyarta da ake ta cacar baki a tsakanin gwamnatin Zamfara da Majalisar Sarakunan da kuma Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro a gefe za aka iya fahimtar cewa mahukuntan kowane bangae na neman su wofantar da irin mawuyacin halin rashin tsaro da irin koma-bayan rayuwa da mutanen jihar suka shiga a kan wannan annoba ta tabarbarewar tsaro a jihar ce. Allah Ya sani yanzu ba lokacin da za a shiga irin wannan cacar baki ba ne. Babban abin da ake bukata bai wuce kowa ya tsaya tsakani da Allah Ya ba da tasa gudunmawar ta yadda za a kawo karshen wannan ta’addanci da ke watsuwa tamkar wutar daji. Irin wannan sakacin na mahukunta da sauran al’umma ya kai shiyyar Arewa maso Gabas da kasa baki daya da kasashen makwabtanmu, yau kusan shekara 10, muna ta fama da annobar Kungiyar Boko Haram.
Gwamnan Jihar Zamfara da Sarkin Anka ya taba janyo hankalinsa a kan lallai ya rika zama jiharsa, shi zai fara wannan jagoranci, sannan sai gwamnatin ta fito da tsare-tsare a kan rawar da take tsammanin kowa zai taka, tare da tabbatar da ana takawar. Mutanen Jihar Zamfara da ma na jihohin Katsina da Kaduna da sauransu da suke fama da wannan annoba su daina tunanin wani maceci zai zo musu daga nesa, su ne macetan kansu da kansu. Allah Ya kama mana, amin summa amin.