Kara wa kwalliyarki armashi da sarka da dan kunne
Kayan kwalliya na sarka da dan kunne da awarwaro da zobe suna da matukar muhimmanci ga mace inda kuma yake kara fiddo da kyawun kwalliyar tata. Idan muka dauki dan kunne za mu ga cewa yana da kashe-kashensa wadanda kuma ake sanya su a lokuta daban-daban. Akwai kanana akwai manya ko mu ce dogaye wadanda […]
Kayan kwalliya na sarka da dan kunne da awarwaro da zobe suna da matukar muhimmanci ga mace inda kuma yake kara fiddo da kyawun kwalliyar tata.
Idan muka dauki dan kunne za mu ga cewa yana da kashe-kashensa wadanda kuma ake sanya su a lokuta daban-daban.
Akwai kanana akwai manya ko mu ce dogaye wadanda kuma ana sanya su ne don su dace da yanayin kwalliyar mace.
Ita ma sarka kamar dan kunne take tana da yanayin kirarta misali akwai wacce take da kwado akwai wacce take a shimfide.
Dukkansu ana sanya su ne daidai da yanayin kwalliyar mace ko mu ce yanayin yankan wuyan rigar mace. Idan dinkin wuyan zagayayye ne za a sa sarka irinta .
Haka kuma idan wuyan mai fadi ne za a iya sa sarka shimfidaddiya.Sai dai shi zobe da awarwaro ba a cika mayar da hankali wajen zabinsu ba.
Ya danganta da irin wanda mace ke sha’awa ko kuma wanda ya yi daidai da hannunta.