karamar Hukumar Guri za ta kashe Naira miliyan 29 don samar da makabarta
Karamar Hukumar Guri a Jihar Jigawa za ta kashe Naira miliyan 29 wajen samar da makabarta ta zamani da gyara hanyar Zugo zuwa cikin garin Guri.Shugaban karamar hukumar, Mlam Haruna Dauda Guri ne ya bayyana wa Aminiya haka ta bakin kakakin karamar hukumar Malam Sunusi A. Doro jim kadan da bayar da kwangilar aikin makabartar […]
Karamar Hukumar Guri a Jihar Jigawa za ta kashe Naira miliyan 29 wajen samar da makabarta ta zamani da gyara hanyar Zugo zuwa cikin garin Guri.
Shugaban karamar hukumar, Mlam Haruna Dauda Guri ne ya bayyana wa Aminiya haka ta bakin kakakin karamar hukumar Malam Sunusi A. Doro jim kadan da bayar da kwangilar aikin makabartar da na hanyar ga wani kamfanin ’yan kasuwa da ke yankin masarautar Hadeja.
Ya ce an ba kamfanin da zai yi aikin makabartar da hanyar Zugo zuwa Guri wa’adin wata shida ya kammala aikin.
Ya ce za a samar da rijiya ta tuka-tuka da dakin ajiye kayan aiki tare da kewaye
makabartar da fitulu na zamani da kafa mata janareta domin inganta yanayin tsaro a makabartar.
Shugaban ya ja kunnen kamfanin da ya yi aiki mai nagarta, kuma muddin aka samu sabanin abin da ke cikin yarjejeniyarsu ba za su amince ba.
Wakilin kamfanin ’yan kwangilar Alhaji Muhammadu Baban Shahada ya ce kamfanin zai yi bakin kokarinsa wajen yin aiki managarci a makabartar tare da samar da ingantacciyar hanya.