Karamar Hukumar Gwiwa ta kashe  Naira miliyan 13 kan bunkasa rayuwar al’umma

A kokarin Karamar Hukumar Gwiwa da ke Jihar Jigawa ke yi don taimaka wa mata da manoma da sauran al’umma, karamar hukumar ta raba wa mutane jarin Naira miliyan 13 da dubu 313 da 450 da nufin dogaro da kansu inda aka bai wa mata 600 jari. Shugaban Karamar Hukumar Gwiwa, Alhaji Sale Ahmed Zauma ne […]

Karamar Hukumar Gwiwa ta kashe  Naira miliyan 13 kan bunkasa rayuwar al’umma

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar

A kokarin Karamar Hukumar Gwiwa da ke Jihar Jigawa ke yi don taimaka wa mata da manoma da sauran al’umma, karamar hukumar ta raba wa mutane jarin Naira miliyan 13 da dubu 313 da 450 da nufin dogaro da kansu inda aka bai wa mata 600 jari.

Shugaban Karamar Hukumar Gwiwa, Alhaji Sale Ahmed Zauma ne ya bayyana haka inda ya ce sun saya wa manoma injunan ban-ruwa don noman rani kyauta da nufin bunkasa noman rani da na damina a yankin.

Ya ce karamar hukumar ta sayi injunan a kan Naira miliyan biyar da dubu 463, kuma ta sayi babura 18 ta raba wa matasa masu sana’ar acaba a kokarin karamar hukumar na ganin matasa sun zama masu dogaro da kansu.

Da yake jawabi, Shugaban Jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma a Jihar Jigawa Alhaji Mannir Uba Gumel ya jinjina wa karamar hukumar saboda namijin kokarin da take yi wajen gina rayuwar mutane.

Dan Majalisar Jihar daga yankin, Malam Aminu Zakari Tsubut ya ce a shirye Gwamnatin Jihar take don aiwatar da ayyukan raya kasa a yankin, saboda haka ya bukaci al’ummar yankin su ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya don samun dorewar dimokuradiyya a Najeriya.