Karamar Hukumar Hadeja ta rufe gidajen giya hudu
Wani kwamiti mai karfin gaske da da karamar Hukumar Hadeja da ke Jihar Jigawa ta kafa ya rufe gidajen giya guda hudu a Unguwar Randa da ke cikin garin Hadeja. Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa Malam Ibrahim dahiru Garki ya tabbatar da rufe gidajen giyar, inda ya ce kwamitin da ya gudanar da aikin […]

Wani kwamiti mai karfin gaske da da karamar Hukumar Hadeja da ke Jihar Jigawa ta kafa ya rufe gidajen giya guda hudu a Unguwar Randa da ke cikin garin Hadeja.
Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa Malam Ibrahim dahiru Garki ya tabbatar da rufe gidajen giyar, inda ya ce kwamitin da ya gudanar da aikin ya kunshi wakilan karamar Hukumar Hadeja da jami’an Hisba da ’yan kato-da-gora da jami’an tsaro na farin kaya (Sibil Difens).
Wata majiya ta ce kwamitin ya rufe gidajen giyar da ke Hadeja saboda karatowar watan azumin Ramadan da kuma kokarin kawo karshen harkokin sha da sayar da giya da kwayoyi a jihar.
Kwamandan Hisbar ya roki sauran shugabannin kananan hukumomin jihar 26 su yi koyi da abin da karamar Hukumar Hadeja ta yi na hana sha da sayar da giya.