Karamar Hukumar Kanam ce kan gaba wajen noman auduga a Filato – Hudu Hamidu
Shugaban karamar Hukumar Kanam dake Jihar Filato, Alhaji Hudu Hamidu Bale ya bayyana cewa karamar hukumar Kanam ce kan gaba wajen noman auduga a Jihar Filato. Alhaji Hudu Hamidu Bale ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi, a wajen kasuwar baje koli ta Jos da take ci a halin yanzu. Ya ce muna […]
Shugaban karamar Hukumar Kanam dake Jihar Filato, Alhaji Hudu Hamidu Bale ya bayyana cewa karamar hukumar Kanam ce kan gaba wajen noman auduga a Jihar Filato. Alhaji Hudu Hamidu Bale ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi, a wajen kasuwar baje koli ta Jos da take ci a halin yanzu.
Ya ce muna noman auduga mai kyau a wannan karamar hukuma, kuma muna noman auduga ba tare da sanya taki ba, domin kasar Kanam tana da taki sosai.
“Audugar da ba a sa mata taki, ta fi tsada ko a kasashen turai. Don haka audugar da ake nomawa a karamar hukumar Kanam za a iya fita da ita zuwa kasashen waje’’.
Ya ce akwai fadamu a wannan yanki, kuma duk abin da aka shuka a karamar hukumar yana yi, don haka manoman wannan yanki suna noman shinkafa da gyero da waken soya da sauran kayayyakin amfanin gona.
Ya ce shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce a koma noma da kiwo ne domin shi ne tushen komai na arziki. Don haka ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar Kanam da Najeriya baki daya su tashi su kama aikin noma.